Daga Abubakar Abdullahi, lafia
A kokarin da take na samar da aikin yi da kuma bunkasa tatalin arzikin jihar, gwamnatin Jihar Nasarawa a karkashin jagorancin Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, tana lalubo hanyoyin hadin gwiwa da wasu kasashen Turai su hudu da suka hada da Sweden, Finland, Denmark da kuma Norway don cimma kudurinta.
Gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya sanar da haka a yayin da ya karbi bakuncin jakadun kasashen hudu a fadar gwamnati da ke Lafia cikin wannan mako.
Gwamnan wanda ya bayyana jin dadinsa kan ziyarar, ya ce kasashen sun kasance a jerin kasashen duniya masu karfafa zaman lafiya a duniya, suna kuma bada gudunmawa a bangarori daban-daban da suka hada da fannin noma da kiwon lafiya da ilimi da gine-ginen, da wannan ya ce zai zama alfanu ga jihar ta yi hadin gwiwa da su.
Al-Makura ya ce, “Daga cikin kasashen, kasa kamar Sweden ta taimaka wa jihar wajen tsara ayyukan hukumar ajiyar bayanan filaye cikin na’urar kwamfuta ta jihar wanda hakan ya kawo cigaba mai yawan gaske a fadin jihar”.
Don haka ya ce gwamnati za ta so kasashen hudu su hada kai da gwamnatin jihar wajen tafiyar da harkokin sabuwar makarantar nakasassu da gwamnatin ta gina, tare da cewa ana sa ran makarantar za ta soma aiki a farkon shekara mai zuwa.
Da suke jawabi, jakadun kasashen Sweden Inger Ultbedt da na Finland Pirjo Suomela Chowhury da Norway Jens Peter Ktempruel da kuma na Denmark Torben Gettermann, duk sun yaba da irin karbar da suka samu. Suna masu cewa, ziyarar tasu ta ba su damar ganin irin abubuwan da jihar ke da su kuma idan sun hada kai da jihar za a ci riba sosai. Duka jawaban bakin sun fi karkata ne zuwa ga fannin noma, inda suka ce hakan zai samar da abinci da kuma sana’o’i ga matasa.
Tun farko a nasa jawabin, jakadan Nijeriya a kasar Sweden wanda dan asalin Jihar Nasarawa ne, Musa Ilu Mohammed, wanda kuma bisa gayyatarsa ce jakadun hudu suka ziyarci jihar, ya ce ziyarar takwarorin nasa ya ba su damar kara sanin Nijeriya da kuma nuna musu irin gudunmawar da za su kara bai wa kasa. Tare da cewa zai yi aiki kafada da kafada da takwarorin nasa domin kawo cigaba ga daukacin kasashen.