Connect with us

Uncategorized

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Raba Tirela 36 Na Abinci – Hon. Maifata

Published

on

Shugaban karamar hukumar Lafia kuma jagoran shugabannin kananan hukumomin Jihar Nasarawa, ALHAJI AMINU MU’AZU MAIFATA, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta raba tirelolin kayan abinci guda 36 ga talakawa, don rage radadin halin da a ka tsinci kai na tabarbarewar tattalin arziki, musamman ma a wannan lokaci na annobar cutar Korona, wacce ta durkusar da al’amuran yau da kullum. Hon. Maifata ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da Wakilin LEADERSHIP A YAU, ZUBAIRU M. LAWAL, inda kuma ya tabo wasu batutuwan da dama. A sha karatu lafiya:

 

Yanzu lokacin damina ne; akwai gurare da yawa da a ke fama da matsalar ambaliyar ruwa a garin Lafia. Wane mataki ku ka dauka?

A gaskiya Gwamnatin jihar Nasarawa ta dauki mataki kan wannan lamarin saboda akwai unguwannin da suke fama da matsalolin so sai wanda hakan yasa Gwamnatin jihar take fadi rashi ganin a samar da manyan hanyoyin ruwa, saboda matsalar zaizayar kasa da muke samu yakan kawo afkawar gurare. Himmar da gwamnatin jihar ta yi ga shi Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu ta taimaka da miliyoyin naira domin a rage matsalolin zaizayar kasa cikin jihar Nasarawa. karamar hukumar ta yi iya bakin kokarinta kuma abin ya sha karfita. Kuma twimakon da Gwamnatin Tarayya ta bada munyi murna Kuma zamuba da hadin kai so sai a nan fannin na karamar hukuma muna yi namu kokari. Kuma yanzu mun nuna guraren da wannan matsalar yafi kamari a karamar hukumar Lafia.

 

Kamar ina da ina ku ke fama da zaizayar kasa a cikin garin Lafia?

Akwai gurin gidan Marigayi Gwani guda ina ake kira rwmin kurw wannan gurin rwmi ne bw karami ba. wanda kuma karamar hukumar Lafia tayi kokari saboda an gyara anyi gada a wurin. Amma yanzu guraren da ake fama da matsalolin akwai wajen GSS maina idan kaje ta bayan gurin zaka gani al’umman gurin suna fiskantar matsal so sai. Haka zalika akwai layin unguwar jaba suma al’umman guraren basu iya barci idan ana ruwa. Akwai a yankin C Dibision, akwai gurare daban-daban a cikin Lafia da suke fama da irin wannan matsalar idan damuna ya fadi basu iya barci.

 

Yanzu mu na cikin damina, ko akwai shirin da karamar hukumar ta yi yunkurin, domin tallafa wa manoma?

Batun harkar noma gwamnatin jihar tuni ta dade da raba Takin zamani garemu mu kuma har mum mikashi ga Manoma. Kuma a karamar hukuma ta ta Lafia akwai tsohuwar tirakto da yake zaune a kasa tsawon shekara bakwai na gyara shi yana aiki, guda biyu ne dayan ma zamu gyara sannan zamu saya maganin gona da zamu rabawa manoma kamar yadda muka raba masu takin zamani.

 

Kan wane farashi a ka raba takin zamanin?

Farashin mai sauki naira dubu biyar, kaga a waje yafi haka. Amma Gwamnatin Nasarawa saboda ta taimakawa manoma domin amfanin gona yayi kyau a kuma sayar da sauki sai ta taimakawa manoma hannu da hannu.

 

A na fama da matsalar annobar cutar Korona. Ko akwai tallafin da gwamnatin jihar ta raba, wanda ya zo ga karamar hukumar Lafia?

Tallafi na farko da jihar ta raba ya iso garemu kuma muna raba shi a matakin gunduma gunduma kuma al’umman gundumomin sun ammafa da wannan tallafin. Yanzu haka akwai kwamitin da nake ciki kuma an gama tattaunawa karkashin Mataimakin Gwamna Dakta Emmanuel Akabe, akwai kayan abinci da ya kai tirela 36 wanda wasu ba adin yan kasuwa suka turo shi zuwa jihar Nasarawa saboda a rabawa jama’a za’araba wannan kayan lungu da sako na cikin jihar Nasarawa saboda al’umma su amfana. Ko wata karamar hukumar ta turo wakilanta wajen rabon wannan kayan abincin. Haka zalika akwai wakilan Sarakuna da wakilan addinai da sauransu.

 

Akwai wasu ayyukan da ku ke yi kuma a na maganar cewa ayyukan da gwamnatocin baya su ka fara ne. Ko me za ka ce?

Ni Ina koyi ne da abinda maigidana Gwamna Injiniya Abdullah Sule ya ke yi. Duk ayyukan da ya samu na gwamnatin da ta shude ya na karasa su. Akwai ayyukan raya kasa da ya samu manya ya kammalasu. Haka muma a matakin karamar hukumar mukeyi. Ai ko ramin kura da nayi magana wata Gwamnati ce a karamar hukumar ta zo da tunanin ayi ta tafi ba a yi ba ni kuma da na zo na yi. Akwai ayyuka da yawa da na gada daga tsohon Shugaban karamar hukumar kuma na kammala. Sannan akwai ayyukan da na kirjiresu kamar guraren Shan magani dake wasu anguwanni, duk mun kammala ayukansu. Sannan akwai gyaran makarantu da sanya kujeru da sauransu kuma akwai wasu ayyukan na raya kasa wasu mun kamala wasu bamu kammala ba amma muna kai.

 

A yanzu a na samun matsaloli na yawaitar fyade. Ko akwai matakin da ku ka dauka kan masu aikata wannan laifi?

Tuni mun dauki matakai na dakile irin wannan mummunar lefin. Daga cikin matakin da aka dauka ne ya kai ga an kama wanda yayiwa yar wata uku Fyede. Don daga lokacin da mu ka samu wannan labari da mu da matar Mai Girma Gwamna, Hajiya Silifat Abdullah Sule, mu ka hada kai a ka kira duk jami’an tsaro da bangaren yan sintiri aka sanya idanu aga an kama wanda ya aikata wannan mummunar aiki, kuma cikin ikon Allah aka kamashi. Kuma daya-bayan-daya duk za a kama masu wannan mugun aiki a hukunta su.

 

Ina batun aikin gina tashar mota ta zamani, wacce a ke ginawa cikin karamar hukumar Lafia?

Mu wannan aikin mu za mu amfana da shi, saboda wannan filin na karamar hukumar Lafia ne kuma yanzu haka aiki yana tafiya sosai. Mu na bada hadin kai da goyon baya, domin cigaban al’ummar jihar Nasarawa ne daga ko’ina.

 

Ina sakonka ga al’ummar Jihar Nasarawa?

Sakona shi ne, mu bai wa gwamnatin hadin kai mu zauna lafiya saboda babu abinda yafi zaman Lafiya dadi. Idan muka zauna lafiya Gwamnanmu Injiniya Abdullah Sule zai samu dama ya yi ma na ayyukan cigaba, wanda kowa zai amfana. Sannan ya kamata mutane su rika bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen bayyanar da masu laifuka duk inda a ka same su. Gwamnatin jihar za ta hukunta duk wanda a ka samu da laifi ko wani iri ne.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: