Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Neja Ta Alwashin Gyara Da Inganta Tsohon Asibitin Tungan Magajiya

Published

on

Shugaban karamar hukumar Rijau, Hon. Bello Bako, Mayanan mai sudan ya bada tabbacin gwamnatin jiha ta himmantu wajen gyaran tsohon asibitin Tungan Magajiya wanda aka gina shi tun lokacin mulkin mallaka.

Mayanan mai Sudan ya cigaba da cewar maganar gyaran asibitin Tungan Magajiya ya tsayawa maigirma gwamna a wuya wanda ko zaman masu ruwa da tsaki da muka gudanar yau laraba sai aka cimma matsaya akan wannan aikin, domin hatta dan kwangilar da kamfanin da za tai aikin an amince da ba su dukkan abinda suke bukata.
Idan ka lura ranar 12 ga watan juni gwamnatin tarayya ta ayyana cewar wannan rana ce ta tunawa da dimukuradiyya a kasar nan, to mu al’ummar Rijau dimukuradiyya tayi tasiri ga mutanen mu domin ta haifar mana da fahimtar juna dan da shi muka samu zaman lafiya a tsakanin mutanen mu har yake ba mu damar yin magana da murya daya duk da yawan jama’a mabanbantar harshe, Allah yasa muna zaune lafiya a tsakanin mu.
Tun samun mulkin kai da zuwan mulkin su marigayi Tafawa Balewa ba mu taba samun rikicin kabilanci ko addini ba domin kasar mu itace a zuciyarmu, wanda wannan asibitin da muke maganarta ta Tungan Magajiya itace asibiti mafi tarihi a jihar nan, saboda mayar da hankalin gwamnati wajen gyaranta babban nasara ce a mulkin dimukuradiyya.
Dan gane da matsalar tsaro kuwa, a ‘yan watanni baya karamar hukumar ana ganin kamar ‘yan ta’adda na neman matsugunni a wajen, amma bisa taimakon maigirma gwamna da jami’an tsaro mun samu nasarar kawar da wannan zargin, domin jami’an soja na barikin Kontagora da Zuru ta jihar Kebbi sun taimaka mana wajen yin sintiri a yankin mu wanda duk wani abinda ake zargi ko fargabansa mun kawar da shi a zukatan al’ummar mu, wanda kasancewa na mai rike da sarautar gargajiya ya ba ni damar samun kan sarakuna inda muka yi aiki ba dare ba rana wajen toshe duk wata kafar da za ta baiwa ‘yan ta’adda dama a kasar Rijau, ka ga wannan nasara a mulkin dimukuradiyya ga al’ummar mu.
Mataki na biyu da muka dauka, idan mun samu rahoton saukar baki da ba mu gamsu da su ba komai dare, komai rana mu kan tabbatar ba mu ba su matsugunni ba, domin ba mu da wajen ajiye baki balle baragurbi ya samu damar labewa dan cin ma nufinsa.
Domin irin yadda ka ke ganin gari ko magidanta sun kwaso sun fantsamo cikin jama’a, mu a Rijau ba mu yarda da wannan ba, mu kan same su mu ji inda suka fito da dalilin shigowarsu wanda a karshe ko mu mayar da su ko kuma mu raka su, su bar mana yankin mu wannan abin ya taimake mu gaya wajen dakile kafofin da batagari ke anfani da shi wajen shigowa jama’a wanda wannan shi ake cewa tsaro.
Sau da yawa ka ke ganin mutane su fantsamowa su ce daga Zamfara su ke, wani lokaci cikin dare za ka ga mutane cikin manyan motocin daukar kaya da iyalan su da dabbobin su a zo a jibge mana a cikin daji ba tare da mun san zuwan su ba a gwamnatance wanda duk mun hori sarakunan kasar Rijau akan baiwa baki matsugunni da sunan noma ko kiwo wanda in aka yi rashin sa’a sai ka ga wannan damar ce ke haifar da matsaloli to a kam mun hana wannan ba za mu yarda ba kuma ba za mu amince ba, kowa ya tsaya a gidansa ya magance matsalar da ke damun sa, wasu lokuttan ma mu ke biyan kudaden da za a sake kwashe su zuwa gaba ko mayar da su inda suke, wannan abin ya taimake mu kwarai da gaske.
Galadiman Tungan magajiya yace akwai sabon tsaron al’umma da rundunar ‘yan sanda ta kirkiro, wato Community Policy, yace wannan tsarin yana da anfani kuma yana da illa. Anfaninsa zai taimaka wajen maganin zaman banza ga matasa, domin za ka ga matasan da ba su da aikin yi sun samu aikin yi, kuma sune za su sanya idanu akan duk wani shige da ficen al’umma da duk wasu bakin abubuwa.
Na biyu kuma yana da illa, illar kuwa mafi yawan matasan da mu ke da su yanzu, za ka ga cewar su kansu suna bukatar a sanya masu ido saboda halin da suka samu kansu na shaye-shaye, da yawan su ba su juriyar yanayi su kan su da yawan su akwai gurbatattu, to idan ba a yi hankali ba wajen gyaran tsara ana iya karye wuya.
Wajen daukar jami’an da za su yi aikin nan idan ba a yi hankali ba za a sa son zuciya, za ka ga wadanda ke jagorancin siyasa kowa zai yi yunkurin sanya na shi dan tunanin abinda za a samu, ko yana da kirki, ko bai da kirki.
Haka abin zai tafi ko jagorori ko iyayen kasa kowa zai yi ta yunkurin sanya ‘yayansa ko jikoki ba tare da la’akari da muhimmancin aikin da ake son yiwa kasa ba, a karshe in ba a yi hankali ba wadanda ake tsammanin su kama masu laifi sai su zama su ne masu laifin.
Amma idan za a cire son zuciya ayi abinda ya dace wannan shirin zai taimaka wajen takaita aikata laifuffuka a kasar domin an baiwa jama’a damar sanya idanu akan abubuwan da ke tafiya a tsakanin su, wanda wannan tsarin da shi ne kasar nan ta faro yin watsi da shi ne ya kai mu ga halin da muke ciki yau.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: