Gwamnatin Neja Ta Cigaba Da Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Duk Da Matsalar Tsaro

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Duk da matsalar tsaro da jihar ke fuskanta, gwamnatin Neja ta cigaba da jawo hankalin masu zuba jari dan hada guiwa da cigaban jihar.
Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya bayyana hakan lokacin da ya bakuncin jakadar kasar Indonesia a Nijeriya, mai girma Usra Hendra Harahap a gidan gwamnatin da ke Minna.
Gwamnan yace matsalar tsaro yafi kamari a yankunan karkara, amma muna bakin kokarin mu wajen shawo kan yankunan da matsalolin suka fi kamari.
Gwamnan ya bayyana wa jakadan cewar, a kokarinsa na neman tallafin gwamnatin tarayya shi ne ta shirya aikin da za a kawo karshen ayyukan garkuwa da jama’a a jihar.
Gwamnan yace duk da lamarin yayi kamari, yana kokarin ganin komai ya daidaita.

Exit mobile version