Muhammad Awwal Umar" />

Gwamnatin Neja Ta Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2020 Ga Majalisar Dokoki

Gwamna Abubakar Sani Bello ya gabatar wa majalisar dokokin jihar kasafin kudin ayyukan musamman na shekarar 2020 ga majalisar dokoki da su kai adadin naira N155,459,814,700.12 dan su zama doka.

Wannan nuna karin adadin kudin da aka fara gabatar wa na N7,247,885,151 akan naira N148,211,929,549.12 wanda majalisar ta amince da shi tunda farko.

Kasafin kudin 2020 da aka kaddamar, ana bukatar naira N70,002,224,042.12 ayyukan da ake gabatar wa, yayin da ake sa ran kashe naira N85,457,590,658.00 dan ayyukan musamman a jihar.

Kasafin kudin da aka yiwa lakabi da Kasafin kudi dan ayyukan raya kasa, yana nuni ne da mayar da hankali akan kammala ayyukan da ake cigaba da aiwatar wa ba a kammala ba, musamman wadanda aka kai kashi saba’in da biyar ama aiwatar da su, domin samun nasarar kammala su cikin lokaci.

Bayan sanya hannu a kasafin kudin 2020, gwamnatin jiha tana sa ran mayar da hankali akan aikin ko kammala ayyukan jiha da hanyoyin cikin gari, musamman aikin tagwayen hanyar Minna zuwa Bida da kuma wasu ayyukan da ta sanya a gaba.

Exit mobile version