Muhammad Awwal Umar" />

Gwamnatin Neja Ta Kara Wa’adin Zaman Gida Da Sati Biyu

Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya kara wa’adin hana zurga zurgar jama’a da zaman gida na sati biyu. Gwamnan yace wannan karin wa’adin ya biyo bayan yunkurin gwamnatin ne na kokarin dakile yaduwar cutar Koronabiarus a jihar.
Da ya ke bayani a zaman majalisar zartaswa da ya gudana a gidan gwamnatin jihar kan nasarar kwamitin yaki da cutar a fadar gwamnatin jihar, yace za a baiwa jama’a damar zurga zurga a yankunan su tare da bin shawarwarin masana kiwon lafiya, ta hanyar bada tazara da sanya takunkumin fuska da yawaitar wanke hannaye, wanda duk kuma ya saba za a hukunta shi.
Gwamnan yace ba a amince da zurga zurgar ababen hawa a wannan lokacin na killacewa ba, sai ga masu ayyukan musamman. Amma akwai ranakun da aka ware dan sassautawa jama’a, sune ranakun Talata da Juma’a, da Lahadi, wanda za a iya fita daga karfe bakwai na safe zuwa karfe goma sha biyun dare da zai ba su damar zagawa a cikin yankunan kananan hukumomin su kawai.
Yace ba a amince da duk wani taron buki ko na addini a wadannan ranakun ba.
Ya bukaci dukkanin makarantu da ofisoshi su cigaba da kasancewa a rufe, haka dukkan manyan kasuwanni za su cigaba da kasancewa a rufe sai kananan shaguna da kasuwanni makota, dukkanin shagunan da aka amince su bude da wajajen Ibada dole su tanadi sinadarin wanke hannu kuma su rika anfani da takunkumin fuska, duk wadanda aka samu da saba wannan dokar za a rufe shagon ko wajen Ibadar.
Gwamnan yace duba da yadda cutar ta ke yaduwa ya tilasta takaita zurga zurgar jama’a da ababen hawa.
Yace gwamnatin jiha za ta kara kaimi wajen ganin ba ta bar iyakokin jihar a bude ba domin sanya ido da hana shigowar baki, duk bakon da ya ratso za a killace shi na adadin kwanakin da dokar ta tsara, dan kaucewa yaduwar cutar a cikin jihar.
Gwamnan yace ‘yan kabu kabu zasu dauki mutum daya ne akan mashin, yayin da masu sana’ar tukin Keke-Napep zasu dauki mutum biyu ne kawai kuma wajibi ne kowa yasa takunkumin fuska.
Gwamnan ya bukaci kwamitin sanya ido akan hana yaduwar cutar Koronabiarus ta jiha da ta hada kai da shugabannin kananan hukumomi domin ganin ana bin dokar sau da kafa a yankunan kananan hukumomi.
Ya bada tabbacin cewar gwamnatin jiha za ta shiga zango na biyu na bada tallafi ga mabukata a mazabu 274 ga gidajen da ake kintace su a wannan satin.

Exit mobile version