Muhammad Awwal Umar" />

Gwamnatin Neja Ta Mika Sunayen Mutane 17 A Matsayin Kwamishinoni

Gwamnatin Neja ta mika sunaye mutane goma sha bakwai da take bukatar baiwa mukaman kwamishinoni ga majalisar dokokin jihar

Daga cikin sunayen dai, akwai Mista Emmanuel Umar daga karamar hukumar Shiroro, wanda yana daya daga cikin wadanda suka taka rawa wajen samun nasarar zabukan da suka gabata.

Sai Mista Sunday Kolo, daga karamar hukumar Gbako, wanda tsohon kwamishina ne da ya taba rike ma’aikatar yawon bude ido ta jiha a zangon farko na gwamnatin Abubakar Sani Bello. Sauran sun hada da Hajiya Hannatu Salihu, daga karamar hukumar Lapai, wadda tsohuwar jami’a ce mai kula da bada tallafi da rance ga dalibai a wannan gwamnatin.

Sai Injiniya Ibrahim Panti daga karamar hukumar Labun, wanda ya taba rike mukamin kwamishina a ma’aikatar sufuri kafin daga bisani ya koma ma’aikatar muhalli a zango farko na mulkin nan.

Barista Abdulmalik Sarkin Daji, daga karamar hukumar Mariga, tsohon shugaban karamar hukumar kuma tsohon dan takarar majalisar wakilai da ya gabata, masani shari’a ne kuma matashin dan siyasa.

A cikin sunayen dai akwai, Barista Mukhtar Nasale daga karamar hukumar Bargu, sai Barista Mohammed Tanko Zakari daga karamar hukumar Suleja. Da Alhaji Haruna Dukku wanda ya taba rike mukamin kwamishina a zango farko daga karamar hukumar Rijau.

Muhammad Sani Idris kuwa shi zai wakilci karamar hukumar Tafa a majalisar zartaswa ta jihar. Alhaji Yusuf Suleiman kuwa shi ne zabin karamar hukumar Agaie a cikin sunayen da aka mikawa majalisar.

Sauran sun hada da Dokta Mustapha Jibrin tsohon kwamishinan lafiya daga karamar hukumar Chanchanga, sai Br. Nasara Dan Mallam daga karamar hukumar Wushishi tsohon kwamishinan ma’aikatar shari’a, da Haj. Ramatu Muhammed Yar’adua daga Edati, Hon. Mamman Musa kuwa zai wakilci karamar hukumar Bosso, sai Hon. Haliru Zakari Jikantoro tsohon dan takarar kujerar sanata a yankin Neja ta arewa, sai Dakta Maku Sidi Muhammad, Hon. Zakari Abubakar daga karamar hukumar Munya.

Kwamishinonin ana sa ran zasu fara aiki nan take da zaran majalisar dokokin ta tantance su.

 

 

 

Exit mobile version