Jam’iyyar ADP reshen jihar Neja ta jajanta ma ‘yan kasuwar garin Bida da iftila’in gobara ya kai su ga hasarar dukiya mai dinbin yawa. Shugaban jam’iyar Tanimu Sarki Kwamba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sakatariyar jam’iyar da ke Minna.
Tanimu Kwamba ya cigaba da cewar yana jajantawa al’ummar jihar Neja na rashin sanin inda gwamnatin jiha ta kai naira biliyan dari hudu da tamanin da ta karba daga hannun gwamnatin tarayya da sunan tallafi ga jihar dan biyan hakkokan ma’aikata da ayyukan raya kasa wanda zuwa yanzu ba wanda zai bayar da labarin inda kudaden suke.
Jam’iyyar ta ADP tace akwai bukatar gwamnatin jiha tai bayanin dalilin dakatar da ciyar da dalibai da aka faro duk da makuddan kudaden da aka ware dan yin aikin.
Tanimu Kwamba ya jawo hankalin gwamnatin jiha kan daraja dokar majalisar dokokin jiha akan wa’adin shugabannin kananan hukumomi. Mun san majalisa tayi doka na cikar wa’adin shekarun ‘yan majalisar amma har yanzu mun kasa ji daga ita gwamnatin, a kullun ina ziyartar hukumar zabe koda mun yi tuntube da jadawalin zaben kananan hukumomi wanda yanzu haka mun shirya mai, muna bukatar an sanya lokaci dan mu ma mu gwada sa’ar mu.
Shugaban ya jawo hankalin ‘yayan jam’iyyar da su kara zage damtse nasarar da suke gani ba ta shi ba ce ta jam’iyya ce gaba daya, dan haka ADP a shirye take dan kai al’ummar jihar nan gaci.