Daga Muhammad Awwal Umar,
A yammacin Lahadin nan Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da sanarwar sako fasinjojin motar sufuri ta hukumar NSTA mallakin gwamnatin jihar.
Bayanin hakan na kunshe ne a wata takardar sanarwa da jami’ar yada labaran gwamnan jihar, Mary Noel Berje, ta sanya wa hannu.
Jami’ar ta wara da cewa, dangane da daliban kwalejin kimiyya mallakin gwamnati dake Kagara da ma’aikatan kwalejin da iyalansu kuwa, ana kan tattaunawa da maharan, wadanda su ma za su fito nan bada jimawa ba.
Akalla fasinjoji 40 ne aka yi garkuwa da su a lokacin da maharan suka kai hari ga motar a kauyen Kundu dake cikin karamar hukumar Rafi ta jihar Neja inda aka kubutar da mutum 10 a karshen makon jiya.
Kokarin jin ta bakin wasu daga cikin makusantan mutanen da aka yi garkuwan da su ya ci tura, haka zuwa yanzu ba wani jami’in gwamnati da yace uffan bayan jami’ar yada labaran gwamnan. Rahotanni dai sun tabbatar da cewar an karbo wadanda aka yi garkuwan da su a wani kauyen da aka sakaya sunansa cikin karamar hukumar Munya ta jihar Neja.