Gwamnatin Neja Ta Sha Alwashin Inganta Makiyayar Dabbobi Ta Bobi

Sakataren gwamnatin Neja, Ahmed Ibrahim Matane yace gwamnatin jiha za ta mayar da makiyayan Bobi da ke karamar hukuma Mariga na daya daidai da zamani a kasar nan.

Matane ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar shirin inganta makiyaya (RGP) wanda ya kunshi wajen kiwon dabbobi ashirin da daya a karkashin shirin koyar da kiwo a Afrika wadda wata kungiya mai zaman kanta ta dauki nauyi bisa kulawar Darakta Phyllis Sortor wanda aka yi sashe na biyu a makiyayan Bobi.

A cewar sa gwamnatin jiha ta dauki wannan matakin ne na inganta makiyayar Bobi dan zama daidai da zamani ta yadda zai zama misali ga wasu gwamnatocin jahohi hanyar da za a samar da zaman lafiya da za a iya samarwa makiyaya kebantancen matsugunni da koyar da su yadda za a ayi anfani da kasa wajen inganta ta.

Yace gwamnati ta samar da makiyaya ( Grazing Reserbe) kuma tayi nisa da ayyukan da zasu bunkasa wajen ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa ta yadda zasu inganta wajen.

Ahmed Matane ya jawo hankalin makiyayan da su yi anfani da abubuwan da aka samar yadda ya kamata, ta hanyar sanya idanu yadda ta da ce dan kaucewa lalata su ta hanyar yin anfani da arzikin da ke wurin yadda ya kamata dan samun nasarar da ake bukata.

Sakataren ya nemi shugabannin makiyayan da su sanya ido sosai, su tabbatar duk wani abinda ba su fahimta ba sun tuntubi hukumomi, haka duk wani abinda zai zama barazana ga tsaro su tabbatar sun kai rahoto ga jami’an tsaro cikin lokaci.

Ya ce, harkar tsaro ya rataya akan wuyan kowa, dan haka ya kamata a hada hannu da gwamnati wajen ganin ta cimma kudurinta ta hanyar kulawa da kare rayuka da dukiyoyin jama’a’.

Matane ya yabawa darakta kula da makarantun Afrika, Phyllis Sortor akan kokarin su na goyon baya ga cigaban makiyayu ( Grazing Reserbe) ta hanyar ilmantar makiyaya.

A jawabin sa, babban sakataren ma’aikatar kula da dabbobi da kiwon kifi, Dokta Jonathan Wasa, ya baiwa fulani makiyaya tabbacin cewar wannan gwamnatin bisa jagorancin gwamna Abubakar Sani Bello za ta cigaba da yin ayyukan da za ta inganta rayuwarsu.

Yace gwamnatin jiha ba zata koma baya ba akan shirinta na samar da ruggage ga makiyaya fulani duk da dakatarwar gwamnatin tarayya akan shirin.

A bayaninta darakta mai kula da makarantun Afrika, Phyllis Sortor tace shirin farfado da makiyayu an samu nasararsa a dukkanin duniya, ba maganar samar da abinci ga dabbobi ne kawai ba har da yunkurin kare kasa da tabarbarewa.

Daraktan ta cigaba da cewar inganta makiyayan Bobi shiri ne da ake maraba da shi, Makaranta da kasashen Afrika za ta cigaba da koyar da dubarun kiwo a zamanan ce, domin makiyayu sa samu kulawa mai ingancin da za a iya anfana da su tsawon lokaci.

Sarkin Fulanin Bobi, Ardo Abubakar Ahijo ya nemi gwamnati ta samar karin cibiyoyin kula da dabbobi tare da samar karin burtulla da zai kara kawo masu sauki.

Exit mobile version