Muhammad Awwal Umar" />

Gwamnatin Neja Ta Sha Alwashin Tallafa Wa Ayyukan IFAD A Jihar

Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana ayyukan shirin tallafawa bangaren noma ta kasa da kasa ( IFAD) shiri ne da zai daga darajar tattalin arzikin masu karamin karfi.

Gwamnan ya bayyana hakan lokacin da ya ke karban manyan ‘yan kasuwa da kwararru masu baiwa kamfanoni shawarwari da jami’an shirin bunkasa darajar tattalin arziki na (IFAD) bisa jagorancin Hajiya Fatima Mukhtar Buhari da su ka ziyarce shi fadar gwamnatin jihar.

Gwamna Sani Bello yace IFAD ta yi kokari a jihar, wanda baya bukatar wani bayani dan sanya ido a ayyukanta, yace muhimmancin gwamnati shi ne hada hannu da masu son kawo cigaba domin daga darajar mata da maza manoma domin kawar da talauci a cikin al’umma.

” Gwamnati da masu sha’awar hada hannu da kawo cigaba akwai bukatar su hada hannu dan tallafawa maza da mata marasa karfi dan ganin sun bunkasa harkokin noma wannan ce hanyar yaki da talauci a cikin al’umma.

Gwamnan yace domin samun nasarar ku a jihar nan akan wannan shirin na ku, akwai bukatar ku kara kokari musamman dan la’akari da yadda jihar ta ke, ta hanyar hada kai da ma’aikatar gona da za ta baiwa IFAD siriin abubuwan da ya kamata tafi mai da hankali lokaci zuwa lokaci.

Ya yabawa shirye shiryen IFAD a jihar musamman ganin yadda jihar Allah ya albarkace ta arzikin kasa wanda ba jihar kawai har kasa baki daya na anfana da su, yace zai yi magana da ministan albarkatun ruwa, dan ganin yadda za a bunkasa Dam da ke jihar dan bunkasa noman shinkafa a jihar.

Gwamnan wanda ya baiwa hukumar tabbacin cewar gwamnatinsa za ta cigaba da baiwa shirye shiryen su goyon baya dan samun nasarar da ake bukata, inda ya bukaci sakataren gwamnatin jihar da ya hada hannu da IFAD da kodinetan jihar domin su fahimci juna wajen bada tallafin gwamnatin jihar ga hukumar, domin idan aka baiwa IFAD hadin kai da tallafi za a samu nasara mai dinbin yawa.

Da ta ke bayani ga gwamnan, shugaban sashen kasuwanci da baiwa kamfanoni shawarwari na hukumar IFAD, Hajiya Fatima Muhktar, tace sun shigo jihar ne dan ziyartar wasu kananan hukumomin Wushishi, Bida da Katcha, Kontagora da Shiroro da su ke da wasu ayyukan da ke cigaba a yankunan yanzu haka.

A na shi jawabin, kodinetan shirin IFAD ta jiha, Dakta Matthew Ahmed, ya bayyana cewar yanzu haka suna tallafawa shirin noman shinkafa, rogo a jihar, yace muna tsammanin za a shigo da noman kwara, doya kofi nan bada jimawa ba, wanda yanzu muna aiki a kananan hukumomi biyar a jiha. Wanda sun samu tallafin mu na horarwa ga kananan hukumomin guda biyar.

Dakta Ahmed yace IFAD ta mayar da hankali akan abubuwa uku, inganta darajar harkar noma, kasuwancin abinci da horar da jama’a yadda ake noman, shirin ya samu nasarori da dama a shekaru shida da su ka gabata, ta hanyar samar da gurabun aiki, ayyukan cigaban kasa ta hanyar gina hanoyin karkara,gadoji, ma’ajiyar kaya da ma”ajiyar kaya a kasuwanni da kuma wuraren sarrafa shinkafa da rogo da makamantansu.

Kodinetan na jiha, ya jawo hankalin gwamnatin jiha wajen bada kason ta dan cigaba da ayyukan IFAD a jihar.

Hukumar IFAD, hukuma ce da majalisar dunkin duniya ta kafa musamman wajen bada shawarwarin yadda magance matsalar talauci da yunwa ga al’ummar karkara ga kasashe masu tasowa.

Shirin IFAD zuwa yanzu a na gudanar da su a jahohi tara a tarayyar Najeriya, jihar Neja kuma ita ce ta zama zakaran gwaji a kididdigar hukumar na wannan zangon kamar yadda hukumar ta bayyana.

Exit mobile version