Daga Muhammad Awwal Umar,
Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar Barikin Sale, Kpakungu da wasu unguwanni na zama tamkar wasu yankuna mafi hadari wanda wajibi ne a dauki matakin gaggawa dan duba yanayin tsarin unguwanni dan canja masu fasali.
Gwamnan yace akwai tsari marar inganci da kuma rashin sanya idanu daga ma’aikatu da hukumomin da ke da alhakin kula da cigaban tsarin unguwanni tsawon shekaru da dama, wanda a cewarsa gwamnatinsa za ta yi dubi dan yin gyare gyaren kurakuran da aka yi.
“Akwai kurakurai da aka tafka a baya, kuma ya kamata mu fara gyare gyaren nan yanzu. Koda kuwa zai dauke mu kashe kudade masu yawa, za mu canja fasalin wadannan unguwannin domin mu samar masu hanyoyin da za su iya samun cigaba ta yadda jama’a zasu anfana”.
Gwamna Sani Bello, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake duba wasu ayyukan da ke gudana da wadanda aka kammala a cikin garin Minna, ya umurci hukumar kula da tsaftar muhalli ( NISEPA) da ta gaggauta tsaftace magudanan ruwa saboda fuskantar damanar bana dan kaucewa ambaliyar ruwan sama a wannan shekarar.
Gwamnan ya nuna damuwarsa akan yadda wasu unguwanni da wasu daidaikun jama’a suka mayar da magudanan ruwa wajen zuba bola, inda sau da dama duk wani yunkurin gwamnati na samu koma baya saboda rashin tsawatawa wanda a karshe kuma hakan kan jawo ambaliyar.
” Mazauna unguwannin da daidaikun jama’a ba sa taimakawa ta hanyar toshe magudanan ruwa ta hanyar zuba bola, wanda ya kamata a daina. Ba za mu jira sai lokaci ya kure ba ta hanyar share magudanan ruwan saboda ruwan sama na gab da sauka ba da jimawa ba”.
A karshen duba ayyukan hanyoyin da gwamnan yake yi, gwamna Sani Bello ya nuna gamsuwarsa da yanayin inda aikin ya kai, sai dai ya nemi ‘yan kwangilar da su kara kaimi akan yadda suke gudanar da aikin kuma su tabbatar sun kammala aikin cikin kankanin lokaci.