Muhammad Awwal Umar" />

Gwamnatin Neja Za Ta Kashe Sama Da Naira Miliyan 500 Wajen Zamanantar Da Mayankar Minna

Mayankar Minna

Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya amince da kashe naira miliyan dari biyar da goma sha biyu da dubu dari bakwai wajen gyarar mayankar Minna ta koma ta zamani.
Kwamishinan ma’aikatar dabbobi da kiwon kifi, Alhaji Haruna Nuhu Dukku ya bayyana hakan ga manema labarai a gidan gwamnatin jihar da ke Minna.
Ya ce mayankar Minna da ta kwashe a kalla shekaru hamsin da kafa ta, tana bukatar zamanantar da ita domin daidaita kamar yadda ya dace, wanda yace domin ta cigaba da samar da nama mai inganci daidai da zamani.
Yace zamanatar da mayankan wajibi ne, wanda za a iya yanka dabbobi guda hamsin a yini a cikin garin Minna kawai, domin bada damar samar da lafiyayyen nama da aikin gyaran nama yadda ya dace mai lafiya ba tare da fargaba ba a kullun.
A cewar kwamishinan, a kallan a kowani wata ana yanka shanu dubu daya da dari takwas, tumakai da raguna guda dubu daya da dari biyar da awakai kusan dubu uku a cikin garin Minna kawai.
A hannu daya kuma a wani zaman majalisar zartaswa da aka gudanar a gidan gwamnatin, ta amince da tsugunnar da al’ummar Muregi da Ketso da kananan hukumomin Lapai da Mokwa da anbaliyar ruwan sama ya shafa za a kaahe a kallan naira miliyan dari uku da dari tas’in da takwas da digo bakwai da miliyan dari biyu da tamanin da hudu da digo shida domin samar masu da abubuwan more rayuwa a sabbin matsugunnan.
Kwamishinan sadarwa da tsare tsare, Malam Sani Idris Muhammad ne ya bayyana hakan bayan amincewar zaman na majalisar zartaswar, bayan kudurin da ma’aikatar filaye da muhalli ta gabatar bayan anbaliyar ruwan sama ya daidaita al’ummomin yankuna da dama a jihar.
Yace tsugunnar da al’ummomin a sabbin matsugunnai ya zama wajibi, domin gaba daya anbaliyar ruwan sama ya daidaita su, ya kara da cewar gwamnatin jihar ta samar da sabon matsugunni da al’uumar Muregi da Ketso.

Exit mobile version