Gwamnatin Nijeriya Ta Ba Da Umarnin Kisa Ga Duk Wanda Ya Sake Kawo Hari Fursunanta

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayar da umarnin kisa ga duk wanda ya sake kawo hari gidan gyaran hali (fursuna).

Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya ayyana hakan a yayin da yake duba gidan gyaran hali da ke Ibadan.

Ya ce wajibi ne jami’ai su harbe duk wanda ya sake yunkurin kawo hari har lahira saboda gidan gyaran hali wuri ne dama da ba a wargi.

Aregbesola ya ce kai hari a gidan gyaran hali hari ne ga kasa kuma ba za a sake lamuntar hakan ta faru ba.

“Wuri ne da ba a wargi, duk wanda ya sake kokarin wargaza sha’anin tsaron wannan wuri to sai dai uwarsa ta haifi wani. Kar a bari ya rayu ballanta har ya ba da labari, sai dai wasu su bayar da labari a kansa.

“Kar ku yi harbi a inda wai mutum zai ji rauni, ku yi harbi na kisa. Kar ku yi harbi na nakastawa, ku yi harbi na kisa.” In ji shi.

Nijeriya dai ta sha fama da balle-ballen gidajen yari musamman a ‘yan shekarun nan a yankin kudancin kasar.

Exit mobile version