Gwamnatin Nijeriya Ta Ci Ribar Milyan 196.3 A Tsiminta Na Watan Janairu – DMO

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta samu ribar Naira milyan 196.3 daga sayar da ajiyarta da ta yi a watan Janairu kadai.

Hakan kamar yadda hukumar bin diddigin basuka ta bayyana kenan.

Sakamakon cinikin wanda aka buga shi a shafin hukumar ta DMO, na yanar gizo a ranar Litinin, ya nu na cewa, an sami ribar milyan 73.05 a kan kashi 12.09, da kuma wasu bukatun da za su tabbata har guda 121 a shekarar 2020.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, Naira milyan 123.25, wanda aka yarda da shi a kan kashi 13.09 da kuma wasu da aka samu nasarar su da za su nuna ya zuwa shekarar 2021.

Wannan sayar da ajiyar dai ana sa ran za ta agazawa gibin kudin da aka samu ne a kasafin kudi.

Wannan sayar da ajiyar dai gwamnatin Tarayya ta bullo da ita ne domin taimakawa masu karamin karfi don karfafa su yin tsimi, domin kuma su sami kari a kan tsimin da suke yi a Bankuna.

Duk ribar da aka samu a cikin ajiyar ana biyansu ne a wasu lokuta na musamman, sannnan biyan daukacin kudaden zai zo ne a lokacin da komai ya nuna.

Ajiyar tana da wa’adin tsakanin shekaru biyu ne zuwa uku, a bisa karancin Zubin Naira 5000 da mafi yawan zubi na Naira milyan 50.

 

 

Exit mobile version