Yusuf Shuaibu" />

Gwamnatin Nijeriya Ta Ware Naira Biliyan 10 Domin Samar Da Magungunan Korona

Ma’aikatar kudi ta ware naira biliyan 10 domin samar da magungunar cutar Korona a kasar nan, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire ya bayyana cewa, an ware naira biliyan 10 wajen sayo wa ‘yan Nijeriya magungunan Korona. Mista Ehanire ya bayyana hakan ne wajen taron manema labarai na kwamitin shugaban kasa kan cutar Korona wanda ya faru a ranar Litinin. Ya bayyana cewa, ana tsammanin samun magungunan cutar Korona guda miliyan 10 wanda za a kawo a cikin watan Maris ta shekarar 2021. Ya kara da cewa, Nijeriya ta shiga cikin tawagar kungiyar kasashe yankin Afirka masu neman magungunan cutar Korona, wanda a yanzu haka akwai ire-iren magungunar cutar Korona miliyan 270.

“Ma’aikatar kudi ta tarayya ta ware naira biliyan 10 domin samar da magungunar cutar Korona a cikin kasar nan.

“A saka rai za a samu sami kyakkyawan muhalli da ababen more rayuwa da samun damar zuba jari da kuma samun magungunar cutar Korona huda miliyan 10, wanda za a fara rarrabawa a watan Maris ta shekarar 2021.

“Sakamakon yawan mutanen da mukr da su, muna shirin kara samun wasu magungunan wanda ya kai kashi 50, domin cimma abin da kasar nan ke bukata,” in ji Ehanire.

Ya bukaci ‘yan Nijeriya su kaucewa wadannan mutune da suke ikirarin sayar da magungunar cutar Korona a cikin kasar nan.

“Ina shawartar ‘yan kasa su yi watsi da duk wani ikirarin wasu ‘yan ta’adda. Za a samar da magunguna wadanda za a yi amfani da su wanda ya samu amincewar hukumar kula da ingancin abinci da kuma magunguna ta kasa (NAFDAC).

“Ina shawartar mutane su kula da jabun magunguna, amma a yanzu babu wani magani da kasar nan ta amince da shi. Hukumar bunkasa lafiya matakin farko (NPHCDA) ita ce hukumar da za a amince da duk wani magani a cikin kasar nan,” in ji shi.

Gwamnatin tarayya Nijeriya ta bayyana cewa, za a sami magunguna huda 100,000 na kashe cutar Korona kafin karshen watan Junairun shekarar 2021, wanda za a tabbatar kowani dan kasa ya samu kariya daga cutar Korona. Haka kuma ta bayyana cewa, ana tsammanin kasar za ta iya samun karin magungunan guda miliyan 42 daga baya.

Mista Ehanire ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da samun sababbin mutane masu dauke da cutar a cikin kasar nan, wanda an tabbatar da mutane 10,300 suke dauke da cutar, sannan an guda mutum 50,750 a cikin mako guda daya, wannan ne ke nuna an samu karuwar kashi 20. Ya ce, a duk kullum sai an gwada mutum biyan har zuwa tsawan mako guda wadanda suke dauke da cutar, an samu karuwar kashi 14 idan aka kwatanta da na makonnin baya.

“Jimillar masu dauke da cutar a Nijeriya wadanda aka tabbatar sun kai 110,387 a cikin mutane 1,172,234 wanda aka gwada, wanda ya kai na kashi 9.4. An samu mutum 1,444 wadanda suka kamu da cutar a cikin awanni 24, an kuma samu mutum 77 da suka mutu a makon da ta gabatar wanda yah ade jimillar mutanen da suka mutu sun kai 1,435.

“An samu mutane wadanda suka kai kashi 20 wadanda aka tabbatar da sun kamu da a watar Junairu fiye wanda aka samu a watan Disamba,” in ji shi.

Mista Ehanire ya kara jaddada cewa, raguwar cutar Korona yana da matukar sauki a hannun gwamnati. A cewarsa, gwamnati ta yi matukar kokari wajen bayar da gwaji da ilmantar da mutane da bayar da tazara da sauran magungunan kamuwa da cutar. Ya kara da cewa, sauran aiwatar da mahimman kamuwa da cutar ya rage ne a tsakanin mutane su kula da shi.

 

Exit mobile version