Yusuf Shuaibu" />

Gwamnatin Nijeriya Za Ta Tallata Masu Zuba Jari Na Cikin Gida

Cibiyoyin Gyaran Mota

A ranar Litinin ce, gwamnatin tarayya ta tabbatar wa masu zuba jari na cikin gida Nijeriya za ta tabbatar da cewa, sun bunkasa a bangarori dama wajen gudanar da ayyukansu na zuba jari a cikin Nijeriya.

Ministan kamfanoni da kasuwanci da zuba jari, Adeniyi Adebayo, ya shi bayar da wannan tabbaci lokacin da yake yi wa wakilan cibiyar Daniel Franco jawabi.
Cibayar ta ziyarci minista ne domin samun goyan bayansa wajen samar da cibiyar kasuwanci kiwon dabbobi a Nijeriya. Adebayo ya bayyana bakinsa cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin kokari wajen gabin burikan masu zuba jari ya cika.
Kalaman wanda ya gudanar a garin Abuja ta bakin mashawarcinsa ta fannin yada labarai, Ifedayo Sayo, ministan ya bayyana cewa, ma’aikatarsa tana kokarin bunkasa fannoni wadanda ba na bangaren mai ba. Ya kara da cewa, bisa ingancin tsarin gudanarwa, dole ne mu yi kokarin bunkasa abincimu na cikin gida da kiyon dabbobi domin samun damar ciyar da kanmu da kuma samun kudade daga kasuwancin kasa da kasa.
“Wajibi ne ma’aikarmu ta mara wa wannan cibiya baya domin samun tsarin sumun tsarin na zuba jari wanda zai harfar da hadin kai a tsakani,” in ji Adebayo.
Shugaban kamfanin Rabelat Nigeria Ltd, Ahmed Raji ya bayyana cewa, cibiyar da ta gudanar da tsari ne gudabi wanda ya hada da bayar da horo da kuma wani bangare na kasuwancin kiwon dabbobi. Ya bayyana cewa, horon zai mayar da hankali ne a kan mahimman ilimin kiwon dabbobi da yadda ake gudanar da harkokin kasuwancin kiwo wanda aka bukatar masu kowa su za su zabi fannin da suke bukata na kowon da kuma gudanar da kasuwancin. Raji ya ce, wannan aaiki ne da zai lakume kudade wanda ya kai na naira biliyan biyu. Ya kara da cewa, za a yi amfani da wadannan tsabar kudade wajen gina ofishin gudanarwa da dakin taro da wajen kwana da sauran abubuwan more rayu a cikin wannan cibiya.
A bangaren alfanun wannan, ya bayyana cewa, cibiyar zai taimaka wajen bunkasa kasuwancin noma a Nijeriya, sannan zai samar da ayyukan yi guda 50,000 da magance matsalolin da ke tsakanin makiyaya da kuma manoma.

Exit mobile version