Connect with us

NOMA

Gwamnatin Oyo Za Ta Cigaba Da Bai Wa Noman Tumatir Muhimmanci

Published

on

Daga cikin watan Janairun shekarar 2020, Gwamnatun jihar Oyo zata fara rabar da Ledar irin noman Tumatir guda 10,000 ga Maboman Tumatir dake a daukacin kananan hukumimin jihar guda 33 da ke a jihar.

Rabar da kayan a cewar Kwamishinan Ma’aijatar Noma da Albarkatu na jihar Mista Jacob Ojemuyiwa gwambatun ta yi hakan ne da nufin kara noma Tumatir a daukacin fadin jihar ta Oyo da kuma rage yawan dogarin da jihar take yi wajen samun Tumatir daga Areacin Nijeriya.

Kwamishinan Jacob Ojemuyiwa ya sanar da hakan ne a yayun da ya karbi Ledojin Irin Tumatir guda 10,000 a matsayin gudunmawa daga gun wata kungiyar aikin noma ta kasa da kasa da ake kira GESA Portal International.

Jacob wanda ya karbi bakuncin kungiyar a Sakatariyar Ma’aijatar dake a garin Ibadan ta jihar ya kuma yi nuni da cewa, rabar da jayan ba wai zasu bunkasa noma a jihar kadai bane harda kuma habaka fannin tattalin arzikin jihar da kuma karwa Maniman na Tumatir.dake a daukacin kanannan hukumin jihar kudin shiga mai yawa.

A cewar Kwamishinan Jacob Ojemuyiwa, “Na gayyaci Malaman aikin gina na OYSADEP da Daraktocin fannin noma don sanar dasu cewar, daga farkin wannan watan, zamu rabarwa da Maniman Tumatir dake a kananan hukumomi guda 33 domin wannan yana daya daga cikin alkawarin da gwambatin jihar ta dauka na bunkasa fannin aikin nima a jihar.

Da ta ke mika Ledojin Irin na Tumatir Jami’a a kungiyar ta GESA kuma wadda ta jagiranci tawagar.Lara Suleiman ta sanar da cewa, mabufar ita ce din a samarwa da nata da kuma matsa ayyukan yi ta fannonun aikin noma iri-iri.

Ta sanar da cewa, an zab9 jihar ta Oyo ne rabar da kayanmusamman ganin yadda Gwamnatin Gwamnan jihar Seyi Makinde ta mayar da hankali wajen habaka noma a jihar da damar da ayyukan yi don bunkasa tattalin arzikin jihar.

A karshe, ta ce, a saboda hakan ta bai wa jihar tabbacn cewar kungiyar ta GESA wajen bunkasa sana’ar Maniman jihar ta Oyo, nusamman din a kara samar da amfabin gina mai yawa a jihar..

A wata sabuwa kuwa, Hukumar Tsugunar da yan gudunhijira ta kasa NEMA, ta shirya wa ’yan gudun hijira 52 dake a karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi taron bita akan fannin aikin noma.

Taron na kwana biyar ne kan dabarun noma na zamani tare da raba musu kayayyakin aikin noma da suka hada da taki da irin shuka da injinan ban-ruwa da na feshi don su dogara da kansu.

A nasa jawabi a wajen rufe taron bitar, Kwamishinan Hukumar Tsugunar da yan gudun hijira ta kasa NEMA, Sanata Bashir Garba Muhammed ya ce saboda damuwar da Gwamnatin Tarayya take nunawa kan halin da yan gudun hijirar suke ciki ya sanya ta shirya wannan bita, don tallafa musu.

Ya ce halin da yan gudun hijirar su ke ciki, bai dace a ci gaba da kawo musu shinkafa da garin kwaki suna ci ba, inda ya kara da cewa, ya fi dacewa a tallafa musu a koya musu noma irin na zamani, domin su dogara da kansu.

Kwamishinan wanda Mataimakin Darakta a Hukumar, Mista Akintunde Oyasanya ya wakilta, ya yi kira ga ’yan gudun hijirar su yi amfani da kayayyakin noman da aka ba su, unda ya kara da cewa, idan suka yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata, gwamnati za ta kara tallafa musu.

A jawabin shugaban ’yan gudun hijirar na karamar Hukumar Toro, Alhaji Abdullahi Musa Garkuwa ya yi godiya ga hukumar da Gwamnatin Tarayya, kan wannan tallafi da aka ba su na horar da ’yan gudun hijirar.

Ya ce babu shakka hukumar tana kokari wajen tallafa wa ’yan gudun hijira, domin baya ga wannan tallafin noma, kwanaki ta turo a zo a yi rijiyoyin burtsatse guda bakwai, a wuraren da ’yan gudun hijira suke zaune a karamar hukumar.

Ya ce akwai ’yan gudun hijira sama da dubu 21 a karamar hukumar, wadanda suka fito daga jihohin Bauchi da Filato da Kaduna da Nasarawa da Yobe da Taraba da Adamawa da Borno, unda kuma ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da sauran kungiyoyi na ciki da wajen Nijeriya, su ci gaba da tallafa wa ’yan gudun hijirar domin su samu su dogara da kansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: