Gwamnatin Jihar Sakkwato ta dakatar da karɓar kuɗin makaranta a dukkanin makarantun sakandare na gwamnati da ke jihar.
Kwamishinan Ilimi na Firamare da Sakandare, Farfesa Ladan Ala, ya ce dole ne dukkanin shugabannin makarantu su daina karɓar kuɗi daga hannun ɗalibai ko iyaye har sai an bayar da sabon umarni.
- Rashin Gyaran Hanya Ne Ya Haddasa Hatsarin Jirgin Ƙasan Abuja–Kaduna – NSIB
- Wa’adin Mulki Ɗaya Kacal Za Ka Yi — ADC Ga Tinubu
An kafa kwamiti na musamman domin duba koke-koken da ake yi kan kuɗaɗen da ake karɓa a makarantu.
Ya bayyana cewa ba a yadda a karɓi kuɗaɗe irin su kuɗin PTA, kuɗin shiga makaranta, kuɗin takardar shaidar kammala karatu, kuɗin MSS, kuɗin shaidar BECE, takardun rubutu, fom ɗin tantancewa, kuɗin SSCE da kuma kuɗaɗen shaidar NECO/NABTEB/NBAIS ba a halin yanzu.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Ibrahim Mohammad Iya, ya garg5adi shugabannin makarantu cewa duk wanda ya saɓa wa wannan umarni zai fuskanci hukunci nan take.