Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta mayar da makarantun Kur’ani dubu hudu zuwa makarantun ilimin zamani domin kara adadin yawan dalibai masu shiga makarantun furamare.
Kwamishinan Ma’aikatar Ilimin Firamare da na Sakandare, Dakta Muhammad Jabbi Kilgori ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a yayin da yake ziyarar duba daya daga cikin makarantun a garin Takatuku da ke Karamar Hukumar Bodinga.
Ya ce an riga an kaddamar da kwamitin Sarakunan Gargajiya a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar kan wannan shirin.
Kilgori ya bayyana cewar shirin agajin gaggawa da Gwamnatin Sakkwato ta kafa yana haifar da da mai ido ta hanyar gine- gine, samar da malamai da sauran agaji da dama.
Ya ce an tura malamai a makarantu a garuruwan da suke zaune domin su magance matsalar rashin zuwa aiki.
Kwamishinan ya kara da cewar Gwamnati ta samar da gine-ginen da za a fadada zababbun makarantun wadanda za su bayar da ilimin addinin Musulunci da darussan ilimin zamani a hade.
Tun da fari, Shugaban Makarantar, Sa’idu Nata’ala ya bayyana cewar makarantar ta na da dalibai 64 wadanda shekarun su suka kama tsakanin shida zuwa 12 wadanda ke karbar ilimin Kur’ani da na zamani.
Daga nan ya bayyanawa Kwamishinan cewar UNICEF ta bayar kayan aiki ga makarantar domin tallafawa shirin. Haka ma Shugaban Makarantar ya yi korafin rashin wadataccen muhallin da za a fadada makarantar domin a cewarsa suna bukatar karin gine-gine da kayan aiki.