A bisa ga hobbasar kwazon inganta haraji da samar da karin kudin shiga; Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kaddamar da shafin yanar gizo da za a rika biyan haraji a saukake a kokarin da take yi na fara biyan albashin ma’aikata daga harajin da take tarawa a 2023.
Kwamishinan Kudi na Jihar Sakkwato, Hon. Abdussamad Dasuki ne ya bayyana hakan a taron horas da sababbin Ma’aikatan Hukumar Tattara Haraji ta Jiha a yau a Cibiyar taron Kasa da Kasa da ke Kasarawa.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta samu gagarumin ci-gaba a sha’anin karbar haraji tun bayan zuwan Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal a 2015, tare da ayyana ta a matsayin mafi kwazo a tattara haraji.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewar Gwamnatin Sakkwato ta kaddamar da shafin musamman na yanar gizo na Hukumar Tattara Haraji wanda jama’a za su rika shiga ko daga gida ne domin biyan harajin su a duk lokacin da suke bukata.
Hon. Dasuki ya yabawa tsarin daukar sababbin ma’aikatan Hukumar Tattara Haraji da aka yi a bisa cancanta ba tare da siyasa ba da manufar kara bunkasa ayyukan Hukumar domin samar da ci-gaban da ya kamata a kokarin da suke yi na ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
“Nasarar da muka samu ta zama na daya a Nijeriya bakidaya a shirin Gwamnatin Jiha na tsaftace tu’ammali da kudi (SFTAS) tare da samun naira tallafin naira biliyan takwas wato dala miliyan 22 daga Bankin Duniya ba aiki na ba ne ni kadai, aiki ne ‘yan kwamiti bakidaya wanda kuma za mu ci-gaba da jajircewa da daura damara domin kaiwa ga gaci.”
Dasuki ya bayyana tabbacin da yake da shi kan sababbin ma’aikatan za su gudanar da aiki da kwarewa da jajircewa tare da cewar za a rika biyan su kudaden alawus a bisa ga kwazon aiki su a wa’adin da aka dora su a watanni uku na farko. Ya ce yana da tabbacin za su cimma wa’adin biyan albashi daga haraji a bisa ga tsalkake tsarin da aka yi a shirin Gwamnatin Jiha na tsaftace tu’ammali da kudade.
Babban bako mai jawabi, Cif Oseni Elemah, tsohon Sakataren Hukumar Haraji ta Kasa ya nuna jin dadinsa kan ci-gaban da Jihar Sakkwato ta samu wajen tara kudaden haraji tare da bayyana farin ciki kan gagarumar nasarar da Jihar ta samu na tallafi daga Bankin Duniya a bisa ga ingantaccen shirin Gwamnatin Jiha na tsaftace tu’ammali da kudade (SFTAS)
Cif Elemah wanda tsohon Shugaban Hukumar Tara Kudin Haraji ne na Jihar Edo, ya bayyana cewar irin wannan kwazon yana dorewa ne kawai da bunkasa ta hanyar hadin guiwa da aiki tare. Ya ce yana da kyau a bayar da fifiko wajen fadakar da al’umma kan muhimmancin biyan haraji domin a kashin kansu su rika sauke nauyin da ke kan su.