Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
Domin baiwa ma’aikata damar mallakar muhalli na kashin kansu, kwamitin da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kafa kan sayar da gidajen Gwamnati ya bayar da shawarar sayar da gidaje 1500 a wurare da dama a fadin jiha.
Shugaban kwamitin kuma Kwamishinan Filaye da Gidaje, Bello Abubakar ne ya bayyana hakan a yayin da yake mika rahoton kwamitin ga Gwamna Tambuwal.
“Kamar yadda binciken mu ya nuna akwai gidaje 1, 497 mallakar Gwamnatin Jiha a unguwanni daban-daban da suka hada da Guiwa, Bado, Arkilla Nasarawa, Runjin Sambo, GRA ta Gabas da ta Yamma.” A cewar shugaban kwamitin.
Abubakar ya bayyana cewar kwamitin ya baiwa Gwamnati shawarar wadanda za su amfana da sayen gidajen su kasance ‘yan asalin jiha wadanda ke aiki a jiha ko Kananan Hukumomi.
Ya kuma ce za a bayar da kulawar musamman ga’ ‘yan asalin jiha da ke aiki a Gwamnatin Tarayya da kuma wadanda ba ‘yan jiha ba da ke aiki da Gwamnatin jiha.
Da yake bayani bayan ya karbi rahoton kwamitin, Gwamna Tambuwal ya bayyana cewar Gwamnati ta tsara amfani da kudaden da aka samu bayan sayar da gidajen wajen kammala sababbin rukunin gidaje da Gwamnatinsa ke ginawa a cikin Birnin Jiha.
“Na gode da kwazon da kuka nuna a wannan aikin. Majalisar Zartaswar Jiha za ta zauna ta tattauna kan rahoton domin amincewa.” Inji Gwamnan.