Gwamnatin Spain ta dauki matakin maida ilahirin ayyukan ‘yan sandan yankin Catalonia karkashinta, domin hana gudanar da zaben raba gardamar da gwamnatin yankin ke kokarin gudanarwa, a ranar 1 ga Oktoba mai zuwa.
A halin yanzu Diego Perez gwamnatin Spain ta nada a matsayin shugaban rundunar ‘yan sandan yankin na Catalonia, matakin da gwamnatin yankin ta ce ba za ta amince da shi ba, domin kuwa karara hakan kutse ne bisa tafiyar da al’amuranta.
An dai sake tura dubban jami’an ‘yan sanda zuwa yankin, tun bayan da kotun kolin kasar ta Spain ta yanke hukuncin haramta kada kuri’ar raba gardamar, bisa neman ballewar yankin na Catalonia.
Sai dai bisa dukkan alamu har yanzu shugabannin yankin na kan bakansu duk da kamen da dama daga cikinsu da ‘yan sandan Spain su ka yi a makon da ya gabata.