Gwamnatin Taraba ta dauki matakan haramta hawan babur kowane iri a fadin Jalingo, babban birnin jihar, da kuma takaita zirga-zirgar babura masu kafa uku da aka kira da Keke Napep daga karfe 6 na safe zuwa karfe 8 na daren kowace rana.
Cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin ta ce dole ce ta sanya ta daukar matakan domin dakile karuwar aikata miyagun laifuka a Jalingo.
- Gwamnatin Filato Ta Sanya Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Mangu
- Gwamnatin Legas Ta Rufe Wasu Kasuwanni Saboda Rashin Tsafta
Mahukuntan sun kara da cewar dukkanin wanda aka samu da laifin karya dokokin zai gurfana a gaban kotun tafi da gidanka da aka kafa.
Matsalar tsaro dai ba sabon abu bane a jihohin Arewacin Nijeriya da dama, kama daga Arewa Maso Yamma, inda ake fama da ta’addancin masu sata da garkuwa da mutane, zuwa yankin Arewa Maso Gabas da suke fama da mayakan Boko Haram.
A Jihar Adamawa da ke mawaftaka da Taraba dai har yanzu dokar hana hawa babura ba ta daina aiki ba a fadin jihar.