Abubakar Abba" />

Gwamnatin Tarayya Ba Za Ta Zura Ido Ta Bari Gadar Neja Ta Rubza Ba –Fashola

Ministan ma’aikatar wuta da ayyuka da kuma gidaje Babatunde Raji Fashola ya sanar da cewar, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba za ta zura ido ta bari gadar Nija da aka gina ta a 1950 ta rubza ba.

Fashola ya sanar da hakan ne a lokacin ran gadin da ya kai akan gyaran da ake kan yi da kula da gadar da ake yi akan gadar, inda ya kara da cewa, gwamnatin tarayya tana sane da cewar, gadar ita kadai ce ta rage da take hada yankin Yamma maso Arewa wadda kuma take taimakawa kasar nan wajen hada-hadar kasuwanci,  a saboda haka gwamnati baza ta yi

sakaci wajen faduwar gadar ba.

Ministan wanda ya bayyana hakan ta bakin Darakta na manyan hanyoyi da zanen gadoji Injiniya Adetokunbo Sogbesan yaci gaba da cewa, gwamnati ta kara mayar da kaimi don cike ginshikin gadar da take fuskantar matukar kalubale  na zai zayar kasa da kuma canza notika da sauran kayan da ake bukata.

Ya kara da cewa, gadar wadda itace ta biyu, ta na da kilomita 1.59 na fadi kuma ta hada da sassa guda hudu na titin Asaba data Toll Plaza, da ta titin Onitsha.

Fashola ya yi nuni da cewa, gadar tana da sassa biyu wadan da aka sanya su a cikin jerin gadoji da aka tsara a kauyen Amakom jihar Delta da kuma a Atani cikin jihar Anambra da kuma aikin mahada dake yankin Obosi a cikin garin  Onitsha-Owerri.

Exit mobile version