Zubairu T M Lawal" />

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dinkin Duniya Za Su Shawo Kan Matsalar Hamada A Nijeriya

Shugaban majalisar Dinkin Duniya, Mista  Antonio Guterres ya ce, suna iya kokarinsu wajen rage zaizayewar Hamada a fadin Duniya. Ya bayyana hakan ne a wurin taron zaizayewar Hamada na Duniya da aka gudanar.

Ya ce, fiye da shekara 20, bangaren da ke kula da zaizayewar Hamada suke gudanar da aiki a kan abin da ya shafi matsalar Hamada, kuma sun sami kwarewa sosai a kan fannin, a inda suke taimakawa duk wani yanki da matsalar Hamada ta shafa.

Ya ci gaba da cewa, a bana dai an kira wannan rana da taken ‘Ranar kare muhalli’ wanda kuma ake sa ran kowace kasa ba za a tafi a bar ta a baya ba, a kan wannan yaki da yanayin gurbacewar Hamada.

Ya bayyana cewa, yawancin kasar da suka fi fadawa wannan hatsari na Hamadan su ne kasashen da suka fi fama da yake-yake, kuma abin yana shafan Al’umman yankin sosai.

Ya kara da cewa, zaizayar hamada yana haifar  da mummunan yanayi a waje. Abubuwa da dama suna haifar da zaizaiyar Hamada, saboda yake-yake da ake yi da makamai masu gubu.

Da yanda ake kona gidaje da kasa, ake mai da gari ya zama kufayi. Misali yadda yanzu yake faruwa a Arewa maso gabashin Nijeriya.

Yanda ake konekonen garuruwa da sauransu wasu gurare da aka yi amfani da bama-bamai da zarar  an samu ramuka sai ya ci gaba da zaizayewa .

Ya ce; gurbatacciyar kasar da ta kone ba ta amsar shuka ko da an shuka abu a cikinta ba zai tsira ba, saboda illar makami mai guba. Daga nan, ya kara da cewa, akasarin al’umman da ke rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira yanzu ko sun koma gidajensu ba za su yi noma ba.

Kuma gine-gine zai ba su matsala saboda yanda yashin garuruwan suka kone, kuma gari ya zama kufayi shekaru da yawa ba ya amfani.

Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya, ya jinjinawa hukumar Nijeriya saboda yanda suka hada kai da bangaren kula da zaizayar hamada na Majalisar Dinkin Duniya domin shawo kan wannan lamarin da gaggawa.

Exit mobile version