Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Gwamnatin Tarayya Da NLC Za Su Duba Rahoton Karin Farashin Wutar Lantarki Da Mai

by Yusuf Shuaibu
February 3, 2021
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
An Nemi Matakan Gwamnati Su Rage Yawan Mukaman Siyasa Don Zuba Jari A Noma
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnatin tarayya da kungiyar kundugon Nijeriya (NLC) za su zantar da hukunci a kan rahoton karin kudin wutar lantarki da na man fetur a ranar 22 ga watan Fabrairu, wanda kwamitin duba karin wutar lantarki da na man fetur ta fitar a kwanakin baya da suka gabata. Ministan ayyuka da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige shi ya bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida jam kadan bayan fitowan ganawa a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadugo a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Ngige ya bayyana cewa, sun aminshi rahoton kwamitin karin kudun man fetur da wutar lantarki kuma sun amincewa da shi a makon da ya gabata. Ya kara da cewa, kungiyar gwadugo ta bukaci a ba ta lokaci ta yi nazari a kan rahoton tare da cimma matsaya.

“Wanna rahoto ne mai tsauri, akwai bukatar gudanar da bincike a kan rahoton wanda tawagar suka gudanar. Kwamitin duba karin wutar lantarki da na man fetur bai kammala aikinsa ba. Muna ciran cikakken rahoton a mako mai zuwa. A ranar 22 ga wannan wutar da muke cikin za su tattauna tare da kungiyar kwadugo domin zantar da hukunci na karshe,” in ji Ngige.
Rahoton kwamitin karin farashin man fetur da na wutar lantarki wanda shugaban kwamitin,Onochie Anyaoku wanda shi ne tsohon daraktan gudanarwa na matatun mai da kayyade farashin a karkashin kamfanin mai ta kasa. Anyaoku ya bayyana cewa, tun a ranar 16 ga watan Disambar kwamitin ya fitar da ka’idojin da zai bi wajen gudanar da aikinsa tare da fitar da mataki ta yadda hukumar kayyade farashin mai, domin cimma tsaya a kan farashin man fetur ta yadda zai dace faran mai da makwabtan kasashe.
Ya ce, “bisa binciken da muka gabtar a kan farashin man wanda ya dace da abubuwa da kwamitin take bukata ta yadda za a amince da shi gaba daya.
“Hukumar kayyade farashin mai a Nijeriya tana gudanar taro akai-akai a kan farashin mai da sauran masu shigawa da mai wajen tabbatar da tsayayyan farashi, domin ya kawo karshen matsalar farashin mai a Nijeriya.
“kungiyoyin da suke halartar taron sun hada da kungiyar kwadugo (NLC) da kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) da kungiyar ‘yan kasuwar mai da kuma kungiyar masu dakon man fetur, inda ake tattaunawa da su ta hanyar yadda za a kawo karshen matsalolin farashin mai a Nijeriya.
“A halin yan zu dai, PPPRA tana kayyade hanyoyin da za a bi wajen kawo tsari wajen rarraba man da kuma ta yadda za a sayar da shi a ko’ina a fadin Nijeriya. Wannan yunkuri zai taimaka wajen fitar da tsarin da ya dace a Nijeriya da kuma daukan darashi ga farashinb man daga sauran kasahe na duniya.
“Dukkan masu shigo da mai ciki har da kamfanin NNPC za su amince da weammam mataki da hukumar PPPRA ta samar domin tabbatar da an samu tsari mai kyau a wajen farashin mai a Nijeriya. kwamitin gudanarwa na hukumar PPPRA shi ya fitar da wannan tsari domin kayyade farashin.
“Ya kamata gwamnatin tarayya ta tilasta ragi ga masu shigo da mau wajen samun saukin yin canjin naira, domin rage wahalhalun da ake samu wanda zai iya janyo hauhawar farashi idan aka kawo man daga waje.
“Domin bunkasa tsarin ta yadda zai amfani mutane, dole ne a samu tsari mai kyau wajen sadarwa da fadakar da mutane da kuma kayyade ribar da za a iya samu, domin rage matsalolin farashin mai a cikin kasar nan.”

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Amurka Take Kallon Kasar Sin Daidai Yana Da Muhimmanci Wajen Kyautata Hulda A Tsakanin Kasashen 2

Next Post

Dokar Kudade Za Ta Farfado Da Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista Zainab

RelatedPosts

Emefiele

Bunkasa Tattalin Arziki: Nijeriya Na Bukatar Kara Kaimi Wajen Adana Abinci – Emefiele

by Yusuf Shuaibu
1 day ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Gwamnan Babban bankin Nijeriya (CBN),...

Bankuna

Rahoton Bangaren Bankuna Yana Nuna Samun Cigaba Mai Matukar Ma’ana – CBN

by Yusuf Shuaibu
1 day ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Rahoton karshe na Babban bankin...

Gwamnatin Masar

Lantarki: Nijeriya Za Ta Hada Kai Da Masar

by Yusuf Shuaibu
1 day ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya...

Next Post
Kasafin 2021

Dokar Kudade Za Ta Farfado Da Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista Zainab

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version