Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kara wa’adin hade rijistar layukan waya da Lambar ’Yan Kasa zuwa watan Fabrairu na 2021 maimakon karshen wannan wata na Disamba, 2020.
Bayanin hakan ya na kunshe ne cikin wata sanarwar Ma’aikatar Sadarwa mai dauke da sa hannun hadin gwiwa tsakanin Mataimakin Shugaban Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Kasa (NCC) mai Cikakken Iko, Farfesa Umar Danbatta da Darakta Janar na Hukumar Kula da Katin Rijistar ’Yan Kasa (NIMC), Alhaji Aliyu Aziz a jiya Litinin.
Sanarwar ta ce, “Kwamitin Musamman kan Tilasta Amfani da Lambar ’Yan Kasa da na Kula da Rijistar Layuka sun gana a yau (wato jiya Litinin), 21 ga Disamba, 2020
“Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami ne ya jagoranci ganawar, wacce ta kunshi manyan masu ruwa da tsaki na harkae da su ka hada da na hukumomin – NCC, EBC-NCC, DG-NITDA, DG-NIMC, ECTS/ECSM-NCC, Shugaban ALTON, Shugabannin MTN, Airtel, Ntel, Glo, Smile da 9Moble a wajen zaman.”
“An kara wa’adin makonni uku ga masu amfani da layuka da ke da Lambar ’Yan Kasa (NIN) su yi rijista daga 30 ga Disamba, 2020 zuwa karin 19 ga Janairu, 2021.
“An kara makonni shida ga masu layukan da ba su da NIN daga 30 ga Disamba, 2020 zuwa 9 ga Fabrairu, 2021.”
Haka nan, sanarwar ta ce, hukumar NIMC ta yi tanadin kiyaye ka’idojin kula da kamuwa da cutar Korona a lokacin rijistar.
Idan dai za a iya tunawa, Ma’aikatar Sadarwa ta bayar da sanarwar rufe dukkan layukan da ba su da NIN daga 30 ga Disamba, wanda hakan ya haifar da tururuwar jama’a a ofisoshin NIMC da na layukan sadarwa a dukkan fadin kasar, lamarin da ke haifar da wahalhalu ga al’umma.
Matsalar ta haifar da Majalisar Wakilai ta yi kira ga Bnagaren Zartarwa da ya kara wa’adin rufewar.