Daga Abubakar Abba
Babban Sakatare a Hukumar Gwamnan Tarayya da ke kula da bunkksa kasar noma (NALDA) , Prince Paul Ikonne ya bayyana cewa, Hukumar ta samar da dama Da Lita 30,000 na fitsarin Zomo da kashinsa kilogiram 1,000 domin sarrafa su zuwa takin zamani a kasar nan.
A hirarsa da manema labaru a Abuja, Prince Paul ya ci gaba da cewa, fitsarin da kashin na Zamo, za a yi gwaji a kansu a dakin yin gwaje-gwaje, inda ya yi nuni da cewa, tuni wasu masu kiwon Zomayen suka fara cin gajiyar hakan.
Har ila yau kuma Babban Sakatare a Hukumar ya bayyana cewa, Hukumar ta NALDA ta gano guraren kiwon Zomaye a daukacin fadin Nijeriya da aka yi watsi da su.
A cewar Babban Sakataren, Hukumar ta gano hakan ne bayan umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na a mayar da hankali wajen sarrafa takin zamani a cikin kasar nan.
“Mun gano hakan ne bayan umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na a mayar da hankali wajen sarrafa takin zamani a cikin kasar nan.” In ji shi.
Babban Sakataren ya ci gaba da cewa, an gano hakan a jihohi 21 irin su Abiya, Adamawa, Akwa Ibom, Borno, Delta, Ekiti da kuma Kaduna.
Ikonne ya kara da cewa Hukumar ta NALDA tuni ta fara karbar abubuwan da take bukata na fitsarin bisa hadakar da wasu jihohin, inda kuma ya bayyana cewa, an kuma fara farfado da wasu gonakai da aka yi watsi da su a yankin Acharaugo da ke a jihar Imo da suka hada da, guraren yin kiwo 20 guraren da ake sa ran kammala aikinsu a watan Agusta na shekarar 2021.
A jihar Ebonyi kuwa, Babban Sakatarey ya bayyana cewa, Hukumar a yayin sake farfado da gonar kyankayasa da ke a yankin Nkaliki tuni Hukumar ta samar da wani shiri wanda za kafa a gundumomin shiyoyi guda 109 da ke a fadin kasar nan.
“Hukumar a yayin sake farfado da gonar kyankayasa da ke a yankin Nkaliki tuni Hukumar ta samar da wani shiri wanda za kafa a gundumomin shiyoyi guda 109 da ke a fadin kasar nan.”
A cewar Babban Sakataren na Hukumar, tuni an fara gudanar da noman rani kan na Shinkafa a jihohin Adamawa, Neja, Yobe, Taraba da Bauchi, a matsayin na gwaji.