Idris Aliyu Daudawa" />

Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Samar Da Ayyuka –Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta dauri aniyar kawo karshen fatara ne, saboda yadda take sa kudade a hannun mutane masu karamin karfi, da niyyar taimaka masu don du tafiyar da karamar harkar kasuwancin su. Ya ce, fiye da kananan‘yan kasuwa dubu talatin ne a jihar taimaka masu a cikin tsarin gwamnatin tarayya.

Farfesa Osinbanjo ya gana da su ‘yan kasuwar ne a Relief Market dake Owerri a karshen hutun mako, a cikin wasu tsare tsaren shi, da suka sa ya kai ziyarar kwana biyu a jihar, ya bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shirye yake saboda ya bada  gudunmawa ga kananan ‘yan kasuwa wadanda dama sun saba hannu baka hannu kwarya.

Mataimakin shugaban kasar wanda shi ne ya kaddamar da Trader- Money shi ‘’Tsarin wani bashi ne wanda ake ba kananan ‘yan kasuwa bashi,a duk fadin tarayyar Nijeriya. Kamar yadda ake ce shi bashin na kananan ‘yankasuwa ne, wadanda zasu biya bashin cikin watanni shida, bayan haka ne kuma za a kara masu bashin wanda ayafi wancan ba tare da bata lokaci ba. Wannan wani tsari ne na Social Inbestment Programme.

Farfesa Osinbanjo hakanan ma ya kai ziyara tsashar cago ta kasa da kasa mai suna Sam Mbakwe, bayan hakan ma ya kaddamar da asbiti mai gado 200 wanda gwamnatin jihar ce ta gina, aka kuma ba Nigerian Airforce. Ya ma kai ziyara ga shugaban masu sarautar gargajiya na jihar HRM  Eze Samuel Agunwa Ohiri  a fadar shi ta Eze Imo.

Dangane da tashar jiragen dakon kaya mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewar, ita ce ta farko a Nijeriya, ya kuma ce gwamnatin tarayya ce ta amince da gina ita tashar, ita kuma gwamnatin jihar Imo ta gina ta.

Ga dai maganar da ya yi “Zamu ga yadda zamu sa masu zaman kansu, a kuma kawo wasu hukumomin gwamnatin tarayya, saboda tafiyar da ita tashar jirage masu dakonn kaya, saboda kayayyakin da suke ciki na kasa da kasa ne, wannan ma wani muhimmin abin more rayuwa ne, saboda akwai alakar kasuwanci tattare da shi.

Sai kuma maganar asibitimai gadaje 200 wanda aka ba Nigerian Airforce, wanda kuma aka mika ma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo, ya jinjina ma gwamnan jihar Rhocas Okoracha, akan abinda ya kira da sunan bukatar shi ta hadin gwiwa da gwamnatin tarayya, irin wannan hadin gwiwar shine abinda ake so.

Akann al’amarin daya shafi masu sarautar gargajiya mataimakin shugaban kasar ya ce, “ Jihar Imo wani babban misali ne, akan hadin kan da ake da shi tsakanin masu sarautar gargajiya da, sauran gwamnatoci daban daban. Gwamnatin jiha da majalisar sarautun gargajiya sun nuna yadda gwamnatocin da suka bambanta suke aiki, saboda al’ummarsu su ci gaba. Abinda nake gani nan ya wuce misali, ba na tunanin koda akwai irin wannan fada a Nijeriyya, inda masu sarautar gargajiya za suyi dokokin da zasu taimaka wajen ci gaba da kuma al’amarin zaman lafiya  a jihar.

A jawabin shi gwamna Okorocha ya nuna farin cikin shi cewar mataiumakin shugaban kasa, har zai iya samun lokacin da har zai kwao ziyarar aiki ta kwana biyu, a wannan jiha tamu, idan aka yi la’akari da ayyukan da suka yi ma shi yawa, da suka hada da ziyarar jihohin da ambaliyar ruwa tayi masu barna. Ya kuma kira ga gwamnatin tarayya da cewar ta basu kudade da suka yi amfani dasu wajen ayyukan da suka hada da tashar jirgin sama mai dakon kaya, da kuma sauna wasu ayyukangwamnatin tarayya.

Gwamnan ya ci gaba da bayanin “A jihar Imo mun kirkiro wata gwamnati ta hudu wadda ake kira da sunan Community Gobernment Council, wadda aka kirkiro ta saboda ci gaban karkara da kuma kawo gwamnati duk wani sako da lungiu na jihar Imo. Masu sarautar gargajiya su suka bullo da wannan tsarin ya kuma taimaka wajen canza fasalin jihar.”

Shugaban majalisar Sarakunan gargajiya HRM Eze Samuel Agunwa Ohiri ya, jinjina ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mataimakin shi Farfesa Yemi Osinbanjo, akan matakan matakan da suka dauka ciyar da kasar gaba, ya kuma kara da cewar Sarakunan gargajiya zasu ci gaba da ayyukansu domin ci gaban kasa.

Exit mobile version