Daga Abubakar Abba, Kaduna
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar, tana tsimayin Dalar Amurka Biliyan 80 daga masu zuba jari masu zaman kansu akan ababen more rayuwa tsakanin shekarar 2014 zuwa shekarar 2018.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi da Tsare-tsare, Aliboh Lawrence ya bayyana hakan a taron tattaunawa da masu zuba jari masu zaman kansu da na gwamnati da ya gudana a Abuja akan zuba kudi kan harkar samar da ababen more rayuwa.
Babban Sakataren wanda ya samu wakilcin Daraktan ababen more rayuwa, Lawal, ya ce, Cibiyar samar da ababen more rayuwa ta kasa (NIIMP), tana sa ran masu zuba jarin masu zaman kansu wajen shiga a dama dasu.
Ya ci gaba da cewa, samun cin nasarar zuba jarin da ake tsimayin, yana bukatar yin wani tsari a tsanake da masu zuba jarin zasu samar cimma nasara.
Shi kuwa Shugaban kungiyar Abubakar Mahmoud, ya bayyana cewa kungiyar ta janyo masu zuba jarin ne, saboda hasashen irin muhimiyar rawar da za su taka wajen kokarin gwamnatin tarayya akan kudirin ta na son samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasar nan.
Shugaban, wanda Bello Abdullahi ya wakilce shi a wurin taron, ya yi nuni da cewa, an shirya tattaunawar ce, don samar da hanyoyi masu sauki ga gwamnati da kamfanonin zuba jari masu zaman kansu don su yi aiki kafada da kafada wajen samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasar nan.
Mahmoud ya kara yin nuni da cewa taron har ila yau, zai gano da kuma shawo kan matsalar siyasa da doka da kuma tsaikon da ake samu na cibiyoyi na kirkiro yadda ake samar da ayyukan ababen more
rayuwa da hanyoyi ga kamfanoni masu zaman kansu da kuma kwararru don kawo ci gaba. Ya ce, taron kuma zai tabbatar da an bi ka’ida wajen cimma burin aikin.
Shi kuwa Mai rikon kwarya na Cibiyar sa ido ta samar da ababen more rayuwa (ICRC), Chidi Izuwah, ya yi nuni da cewa, aikin samar da wuta na kasa da ake son samar na Mega Wat 180,000, sai an tashi tsaye
haikan don cimma nasara.
Ya bayyana cewa, abin da aka yanke shawara akan samar da wutar lantarkin ita ce, Mega Wat daya ga mutane 1000.
Chidi ya buga misali da cewa, “idan mun kai yawan al’umma miliyan 180 a kasar nan, ya kamata ne a ce an samar da wutar lantarki ga mutane 180,000.
Ya ce, babban kalubalen da kasar nan take fuskanta na samar da ababen more rayuwa shine, rashin mayar da hankali daga bangaren kamfanoni masu zaman kansu da kuma bangaren gwamnati.
Ya yi nuni da cewa, in har kasar nan tana son ta cimma burin samar da ababen more rayuwa, dole ne canje-canjen ta da da gudanar da dokokinta a mai da hankali a kan su, inda ya ce, ya kuma zama wajibi da a yi
koyi da sauran kasashen duniya da suka ci gaba akan cimma burin.
Ya bayyana cewa, don samun cin nasarar ayyuka, ya zama wajibi gwamnati tayi shahada don kamfanoni masu zaman kansu su mallake su.
Ya ce, “shin muna da cikarkiyar cibiya mai sa ido muna kudin musaya na kasa da kasa da kuma tattalin arzikin kasa dawwamamme?
Ya bada tabbacin cewar Cibiyar za ta yi dukkan abin da ya dace a bisa tsarin doka dan ‘yan kasar nan su samu ababen more raywa da suke bukata.
Shima Manajin Darakta na Bankin samar da ababen more rayuwa (TIB), Adekunle Oyinloye, ya ce bayar da kudi, ya danganta ne akan irin tsare-tsaren na ayyukan PPP.
Ya bayyana cewa, mafi ywancin tsare-tsare da cibiyoyin gwamnati da suke amfani da ayyukan ba gudanar dasu a bsa tsari, inda hakan yake janyo bada dama ga wadanda suka zuba jarin su, su janye da sun ji
wuya.