Sabo Ahmad" />

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Bunkasa Noman Kashu

A kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin kasar nan ta rage dogaro da man fetur ta fusakar tattalin arzikin kasa, yanzu haka tana kokarin bunkasa noma, wanda sakamakon hakan ne ta samar da wani shiri da zai tamaka wa manoman kashu da sauran wasu kayan amfani gona yadda za a samar da su da yawa, kuma a samar da kasuwar da za a sayar da amfanin a kasuwannanin kasashen duniya.

Yunkurin gwamnatin ya kara fito wa fili ne lokacin da Daraktan Hukuma  bunkasa hanyoyin samar da kasuwar kayan gida a kasashen waje Mista Olusegun Awolowo ya bayyana kudirin gwamnatin tarayya na tallafa nomad a samar da kaswar amfanin a kasashen waje.

Daraktan ya bayyana hakan ne a garin Inugu a wajen wani taron karawa juna sani da aka shiryawa manoman kashu da suran masu ruwa da tsaki a kan wasu sassan amfani gonar da ake noma wa domin sayarwa.

Ya ce kashu na daga cikin amfanin gonar da zai taimaka wajen rage dogaron da kasar nan ke yi a bangaren man fetur. Ya ci gaba da cewa a halin yanzu shirin da gwamnatin tarayya ke yin a bunkasa noma na nuna cewa nan gaba kadan gwamnatin kasar na iya ci gaba da gudanar da al’amuranta ko da babu mai.

“Manyan hanyoyin da gwamnatin ta tsara na ganin an rage dogaro da man fetur din su ne inganta samar da kayan cikin gida da bunkasa noma wanda cikin abin da za a ba muhimmanci sosai a harkar noman akwai kashu da mar da kasuwa ga wadannan kayayyaki da amfanin gona a kasuwannin kasashen waje,”.

Daga nan sai  Awolowo din ya nuna muhimmabcin inganta kayan da muke samarwa, yadda duk inda aka kais hi a kasuwar duniya za a tabbatar da cewa, nagari ne, wanda hakan ce za ta bayar da dammar mutane su saya.

“A matakai daban-daban gwamnatoci na bakin kokarinsu na ganin cewa, an samu ingantattun kayayyaki daga Nijeriya, saboda haka sai ya yi kira da babbar murya ga manoman kashu din da su tabbatar da sun noma kashu mai kyau wanda duk inda aka kai shi a duniya ba za a ji kunya ba,” in ji shi.

Ya ce, ganin yadda farashi mai bas hi da tabbas a kasuwannin duniya, wannan babban kalubale ne da manoman kashu da masu harkarsa za su kawo mana karshen wannan fargaba da kullum take damunmu.

Saboda haka ne ma aka ba kowace jiha a fadin kasar nan da ta samar da wani amfani da za ta bunkasa shi, wanda zai maye gurbin man fetur.

Bisa wannan shiri gwamnatin jihar Inugu ta shiga sashun karfafa manoman kashu, yadda za a tallafa musu da hanyoyin da za su habaka nomansa.

Shi ma da yake kara tabbatar da manufar gwamnatin na bunkasa noman kashu Darakta a ma’aikatar aikin gona ta Inugu, Mista Umah Ossi, ya nuna cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa manoman kashun jihar musamman ma da yake Allah ya albarkaci jihar da kasar noman kashu din da ma sauran amfanin gona.

Ya ce, saboda haka ne ma jihar ta zama zakara a dukkan jihohin kasar nan wajen samar da kashu sannan kuma sai jihar  Kogi wadda ke biye da ita. Haka kuma ya ci gaba da cewa, kashu na daga cikin amfanin gonar da ke daga darajar manoman jihar, don haka ya zama wajibi a kan gwamnatin jihar ta kara fadada hanyar da za a binkasa nomansa domin karin samun ci gaban al’ummar jihar da ma na kasa baki daya.

A karshe, wadanda suka halarci taron sun nuna jin dadinsu bisa kara fahimtar da su gudummawar da gwamnati za ta ba su domin karfafa musu gwiwar yadda za su bunkasa sana’ar ta su ta noma, musamman noma kayan da za su sayar.

 

Exit mobile version