Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi na Tarayya ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da a sake komawa makarantu a ranar 18 ga Junairu bayan cimma yarjejeniya da Gwamnoni, Kwamishinoni da sauran masu ruwa da tsaki.
An cimma matsayar ne a wata ganawa tsakanin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Kwamishinonin Ilimi a Abuja.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Arc. Sonny Echono, wanda ya tabbatar da hakan ya ce:
“Mun tattauna sosai tare da gwamnonin jihohi, masu makarantu, kungiyoyin kwadago da na ma’aikata da wakilan daliban. Kuma yarjejeniya ita ce cewa ya kamata mu sake buɗe duk makarantu.