Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Hutun Kwana 3 Don Bikin Kirsimeti Da Sabowar Shekara

Hutun Kirsimeti

Gwamnatin tarayya ta bada hutun bukukuwan Krsimeti, da ranar ‘Boxing’, da kuma sabuwar shekara, ranakun hutun sune Juma’a 25 ga Disamba da Litinin 28 ga watan Disambar 2020, sai kuma ranar Juma’a 1 ga watan Junairun 2021.

Gwamnatin ta janyo hankulan ‘yan Naijeriya kan darrusan da bukukuwan suka kunsa tare da shawartarsu da su kiyaye dokokin yada cutar Korona, Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwar da sakataren dindindin na ma’aikatar Dakta Shuaibu Belgore ya fitar yau Laraba.

A yayin da ya ke taya al’ummar Kiristan Nijeriya da na kasashen duniya murnar bikin Kirsimetin da Sabon shekara, Aregbesola ya bukaci kiristoci da su yi koyi da koyarwar Annabi Isa da wadanda suka hada da Imani, kauna.

Exit mobile version