Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa NERC Umarnin Dakatar Da Karin Kudin Lantarki

Gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar da ke kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC), umurnin dakatar da sabon karin wutar lantarki wanda hukumar ta yi yunkurin yi. Ministan wutar lantarki, Sale Mamman shi ya bayar da wannan umurni a garin Abuja.

A ranar Talata da ta gabata ce, hukumar NERC ta yi yunkurin kara wa masu amfani da wutar lantarki da ke fadin kasar nan karin biyan kuda. Za a yi wannan sabon karin  ne bisa karkasa masu amfani da wutar lantarkin a Nijeriya, wanda aka fara amfani da shit un a ranar 1 ga watan Junairun shekarar 2021. Hukumar ta daura alhakkin karin bisa hauhawar karin farashin kayayyaki a tsakanin kashi biyu zuwa hudu sakamakon canjin kudaden waje. Sai dai kungiyar kwadugo ta kasa ta sha alwashin zuwa yakin aiki idan wannan karin ya tabbata, wanda ta bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya da duba halin da ‘yan Nijeriya suke ciki a yanzu, wanda hakan  ma ya saba a kan yarjejeniyar da ta cimma da gwamnati a wata biyun da syuka gabata a kan karin kudin wutar lantarki.

Amma a cikin kalamun ministan wutar lantarki, ya bayyana cewa an kafa kwamiti a kan karin kudin wutar lantarki wanda kwamitin ne zai tabbatar da karin ko rashin karin idan ya samu nasarar kammala aikinsa. Mamman ya umurci hukumar NERC ta dakatar da wannan sabon karin wutar lantarki har sai kwamitin ta samu nasarar kammala aikinta a karshen wata Junairu.

Ya ce, “’yan kasa suna sane da tattaunawan da ya gudana a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadugo ta kasa a kan karin kudin wutar lantarki a karkashin kwamitin da aka kafa wanda karamin ministan ayyuka da karamin ministan wutar lantarki suke jagoranta. Kwaminin zai kammala dukkan ayyukansa a karshen watan Junairun shekarar 2021.

“Domin tattaunawa da kwamitin karin kudin wutar lantarki, na bukaci hukumar NERC ta dakatar da aiwatar da karin kudin wutar lantarki, daga kashi biyu zuwa kashi hudu har sai kwamitin ya samu nasarar kammala ayyukan da ke gabansa a karshen watan Junairun shekarar 2021.

“Wannan shi zai bayar da damar fitar da sakamako mai kyau daga wajen  kwamiti bisa ayyukan ya  gabatar. Hukumar gudanarwa na wannan kwamitin ya samar da dai-daituwa da wasu dokokin kasuwancin wutar lantarki wanda zai amfana daukacin ‘yan Nijeriya,” in ji minister.

A ranar Alhamis ce, kungiyar masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da sabon karin wutar lantarki a wannan  lokacin da ‘yan Nijeriya ke kokarin farfadowa daga cikin matsin tattalin arzikin da suke fuskanta. Shugaban kungiyar MAN, Mista Segun Ajayi-Kadir shi ya bayyana hakan lokacin da yake mayar da martini bisa umurnin da gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar NERC na dakatar da sabon karin kudin  wutar lantarki a Nijeriya.

Hukumar NERC ta ce, za ta kara kudin wutar lantarkin  ne daga kashi biyu zuwa huku sakamakon hauhawar kayayyakin da take samu sakamakon karin canjin kudaden waje.

Ajayi-Kadir ya kara da cewa, an kwashe makonni uku ana tattaunawa a tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kunshiyar kwadugo a kan karin kudin wutar lantarki.

“Babu wani hikima na kara kudin wutar lantaiki a dai-dai wannan lokaci da ‘yan Nijeriya ke fama da tsadar rayuwa suna kokarin farfadowa, amma ina da tabbacin hukumar kula da wutar lantarki za ta yi nazari tare da dakatar da karin kudaden kamar yadda gwamnatin tarayya ta bayar da umurni.

“Akwai matakan da ya kamata a dauka a kan farashin wutar lantarki, domin yana daya daga cikin abubuwan da zai iya shafar talakawa kai tsaye.

“Duk sakamakon da kwamitin karin wutar lantarki suka fitar, karin kudin wutar lantarki a dai-dai wannan lokaci ba abu ba ne da zai iya haihar wa Nijeriya da mai ido ba ne da kuma bangaren masana’antu,” in ji shi.

Ajayi-Kadir ya bukaci gwamnatin tarayya da ta duba lamarin dakatar da karin gaba daya, saboda duba yanayin yadda ake fama da matsin tattalin arziki da kuma yadda masana’antu za su kasance idan aka samu nasarar aiwatar da wannan karin.

“Akwai masu amfani da wutar lantarki masu tsananin yawa wadanda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu, idan aka aiwatar da wannan kari zai shafi rugujewar harkokin kasuwancinsu a wannan lokaci.

“An samu matsaloli masu yawa sakamakon cutar Korona wacce ta durkusar da harkokin kasuwanci, bai kamata a yi wannan karin wutar lantarkin ba, a dai-dai lokacin da mutane suke kokarin farfadowa daga matsin tattalin arziki.

“Domin haka, yana da matukar mahimmaci a yi watsi da wannan karin,” in ji  shi.

Exit mobile version