Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Kamfanin Google da ya samar da hanyar sadarwa ta WiFi na kyauta a kasuwanin dake kasar nan. Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya yi kiran a jihar Legas a ranar Juma’ar da ta wuce a lokacin da yake bude kasuwar baje koli ta kasa da kasa karo na 32 da ake kan gudanar a jihar.
Ya sanar da cewar, a yanzu muna samar da kirkiran kaya da Kamfanin na Google ya samar, inda aka samar da yin amfani da WiFi din kyauta a wasu wurare dake kasar nan.
Acewar sa, a yanzu akwai tashoshin na Google a yankuna shida na kasar nan da suka hada da, kasuwannin Palms Shopping Mall, Cibiyar Landmark, jami’ar jihar Legas, MM2, tashar jirgin sama, inda ake yin amfani da kwamfuta da kuma a kasuwar City Mall dake a Ikeja.
Ya yi nuni da cewar, a gare mu abin da yafi mahimmanci shine muna kira ne a damar da WIFI din a daukacin kasuwannin dake kasar nan yadda a cikin watanni yan kadan ma su zuwa za su isa zuwa babbar Kasuwar dake garin Onitsha da kasuwar Gbagi dake a garin Ibadan dz kasuwar Kuto dake garin Abeokuta da babbar kasuwar dake Kaduna da ta Sura dake Legas da kuma tashar jirgin sama dake garin Abuja a karshen wannan shekarar.
Acewar Osinbajo, gwamnati tana yi imani. Cewar yin amfani da dimokiradiyya wajen samar da internet a gari da kasuwanni mutane da yawa za su iya yin kasuwancin su da kuma samun bayanai a cikin sauki.
Da kuma yake tsokaci a kan kalubalen shigowa da kuma fitar da kaya daga cikin kasar nan, ya sanar da cewar har yanzu akwai sauran matsala duk da ragin da aka samar.
Acewar sa, a saboda ha kan ne muke yin kokarin ssmar da tsari don magance ha kan ta hanyar kafa zaure na gudanar da fitarwa da kuma shigo da kaya a cikin sauki muna kuma sa ran a cikin yan watanni ma su zuwa, za’a kaddamar da shirin.
Ya sanar da cewar ana samun tsaikon ne daga bangaren ma’aikatu, sassa da kuma hukumomin gwamnatin.
A jawabin sa na maraba tunda farko, Shugaban cibiyar Kasuwanci, masana’antu na baje kolin Mista Babatunde Ruwase ya ce, taken taron na bana shi ne, sada kasuwanci ta hanyar yin kirkira, an kuma zabo taken ne saboda dk mahimmancin yin dangantaka da musayar ra’ayi a tsa kanin yan kasuwa don a habaka dukiya.
Shi kuwa Shugaban kwamitin shirya taron na sashen kasuwanci Mista Gabriel Idahosa, ya bayyana jin dadin sa ne na cewar ma su zuba jari a kasuwar za su amfana sosai.
A karshe ya ce, ma su zuba jarin, za su kara fadada kasuwanci su da kuma kulla huddar cinkiyayya da ma su sayen kayan su.