Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Karin Mata A Harkar Hakan Ma’adanai

Published

on

Gwamnatin Tarayya tayi kira ga matan dake kasar nan dasu shiga fannin hakar ma’adanai don su inganta rayuwarsu.
Karamin Ministan ma’adanai Alhjai Bawa Abubakar ne ya yi kiran a cikin sanarwar da fitar a garin Osogbo a lokacin da yake jawabinsa na gangamin wayar da kai akan fanin na hakar ma’adanai da aka gudanar a yankin Ibodi dake cikin jihar.
Taken taron shine, daukaka fannin hakar ma’adanai don samar da ci gaba kuma wata jami’a a fannin harkokin mata uwargida Hasana Shaaba ce ta wakilci ministan a wurin taron.
Acewarsa, fanin na hakar ma’adanai yana daya daga cikin fannonoi dasuke samarwa da gwamnatin tarayya da kudin shiga, inda ya yi nuni da cewar, gwamnatin ta lura cewrea mata suna da basira akan yadda zau samarwa da kansu kudin shiga ta hanyar rungumar fannin.
Yaci gaba da cewar, wannan yana daya daga dalilin da ya sanya gwamnatin tarayya take bukatar ganin mata sun rungumi fannin, musamman don samarwa da kansu kudin shiga don suma su zamo masu dogaro da kansu.
Minitan ya yi nuni da cewar mata suna jin tsoron rungumar fannin domin suna ganin kamar karin wani nauyi ne musamman ganin cewar su matan aure ne muka iyaye.
Shima a nashi jawabin, Darakta na matsakaitan hakar ma’adanai Mista Patrick Ojeka, ya yi nuni da cewar, hakar ma’adanai fanni ne mai tsoka fiye da ayyuka a fannin kiwon lafiya, ilimin zamni da abinci mai gina jiki da mata suke son su yi.
Ya sanar da cewar gwamnatin tarayya ce ta shirya taron don ilimantar da mata akan rungumar fannin na hakar ma’adanai yadda zasuyi aikin kafada da kafada da maza yan uwansu.
Ita wata kwararriyar ta tuntuba a fannin uwargida Ngozi chi Okorie, ta yi nuni da cewar, mata zasu iya rungumar fannin musamman don su inganta rayuwarsu, inda ta yi nuni da cewar mata basa shiga fannin don wani ra’ayiu na kashin kansu .
A karshe ta ce, zasu horar da mata akan yadda zasu rungumi fannin.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: