Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta shaida cewa, ta na aiki tukuru wajen gina manyan hanyoyi masu tsawon kilomita 13,000km a sassan kasar nan da za su lakume a kalla biliyan 500 kowace shekara na tsawon shekaru uku da ake son samar da manyan hanyoyi masu nisan kilomita 35,000 a manyan hanyoyin gwamnatin tarayya.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ya lura kan cewa da gwamnatocin baya sun maida hankali wajen gina manyan hanyoyi a sassan kasar nan kamar yadda gwamnatin shugaba Buhari ta sanya a gaba da tunin an kammala gina manyan hanyoyi da dama a fadin kasar nan.
Ya na fadin hakan ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida, ya ce sun gaji hanyoyi da dama da ba a kammala aikinsu ba, wanda tunin suka amince da karawa.
“Wasu daga cikin hanyoyin nan an fara aikinsu tun 2007, wasu da dama kuma a 2006, a ma lokacin da gwamnatin ke da hanyoyin samun kudaden shiga, ya dace tun kafin zuwanmu gwamnati wadannan hanyoyin a samu an kammala su. Har ma wadanda jihohi suka yi an ki biyansu kudadensu, dun an bar mana.”
Fashola ya ce gwamnatinsu tana gudanar da nagartattun hanyoyi ne masu kwargo da za a jima ana amfanuwa da su shekaru aru-aru ba wai aiwatar da hanyoyi jika-na-yika ba.