Gwamnatin Tarayya Ta Fara Horar Da Tsaffin Tsageran Neja Delta 30

Akalla tsaffin ‘yan tawayen Neja Delta 30 ne wadanda suka sami afuwar gwamnatin Tarayya, a yanzun haka suka fara samun horo a kan aikin Gona a kwalejin ayyukan gona ta Tarayya da ke Akure, Jihar Ondo.

Hakan yana daga cikin shirin gwamnatin Tarayya na maido da tsaffin ‘yan tawayen cikin al’umma, inda za a koya masu dubarun noma daban-daban ta yanda za su kasance masu dogaro da kansu.

Da yake magana da sabbin daliban, Shugaban kwalejin ta aikin gonan, Dakta Samson Adeola Odedina, ya ce, za a koyawa tsaffin ‘yan tawayen dubarun noman zamani ne kala-kala, ta yadda za su amfanar da kansu da kuma al’umma.

Shugaban kwalejin, ya ce, sabbin daliban sun zabi sashen da ya fi kowanne kawo kudi ne a aikin gonan, domin sun zabi da su kiwata aladu ne.

Ya kuma bukace su da su yi amfani da gogayyan da suka samu a baya wajen ayyukan sunkuru, yanzun su musanya ta da aikin Noma tukuru, inda ya bayyana masu cewa, kwatankwacin hakan ne Sojojin Nijeriya suke kwatantawa, wajen amfani da jarumtarsu a ayyukan gona.

Shugaban ya kuma yabawa Ma’aikatar aikin gona ta kasa, a kan irin gudummawar da take baiwa kwalejin, ta hanyar samar mata da hanyoyin saukake ayyukan nata masu yawa. yana mai cewa, Jajircewa muke nema a kan abin da ya shafi harkar na Noma a kasarnan, domin bunkasa tattalin arzikinmu cikin hanzari.

Exit mobile version