Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Shinkafa Ga Masana’atun Da Ke Sarrafa Ta

Iyakokin

Daga Abubakar Abba,

Biyo bayan ci gaba da hauhauwan farashin kayan abinci a daukacin fadin Nijeriya, Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a fitar da Shinkafar da ake noma wa a kasar don tura ta ga masu sarrafa ta a kasar.

 

Shinkafar, na daga cikin bashin kayan aikin noman da gwamnatin ta karbo daga gun kungiyar manoman Shinkafa ta kasa (RIFAN).

 

A jawabinsa a yayin kaddamar sayar da Shinkafa ga masu sarrafa ta na kakar noma bana  a garin Bida, a jihar Neja Jami’in RIFAN a jihar ta Alhaji Idris Usman Jakanta ya sanar da cewa, an fitar da ita ne ga masu sarrafa domin a rage ci gaba da hauhawan farashin ta da  sauran kayan abinci a kasuwanni.

 

Alhaji Idris Jakanta ya ci gaba da cewa, za kuma a  rabar da Irin Shinkafar da sauran kayan aikin gona ga manoma nan ba da jimawa ba, inda ya kara da cewa, manoman da ba su biya bashin da suka ci ba, ba za su  amfana da sabon bashin ba.

 

A cewar Jakanta, a karkashin babban bankin Nijeriya CBN, mun kaddamar da sayar da Shinkafar ta cikin gida ga masu sarrafa ta, inda ya bayyana cewa, za a kuma ci gaba da sa ido a kan masu sarrafa ta domin a tabbatar da an kyade farashin ta a kasuwannin kasar nan.

 

Jami’in  ya bayana cewa, za mu iya kiyaye farashin ta a kasauwa ne kawai idan an karfafa kyade farashin ta, musamman domin a dakile ayyukan masu boye ta, inda ya kara da cewa, in har CBN ya gano masu boye ta, zai kulle masana’antun su, a cafke su a kuma hukunta su don hakan ya zama izina ga masu yunkurin mai -maita hakan.

 

Jakanta ya sanar da cewa, bashin da CBN ya karbo daga gun manoman Shinkafar, zai kai taimaka wajen samar da tan 20,000 zuwa tan 30,000 na Shinkafa yadda za su samu damar sayar da ita a kasuwanni.

 

Ya shelanta cewa, a kakar aikin noman ta bana, za a kara  janyo kananan manoma da dama, musamman don CBN ya samu damar cimma bukatar da ya sa a gaba ta wadata kasar da abinci,  kari da  samar da ayyukan yi.

 

Ya bayyana cewa, a kakar noman ta 2021, an tsara tare da kuma tantance sama da kadada 700,000, wadanda daga ciki, za a noma kasa da kashi 20 a cikin dari na kadadar  tuni, CBN ya amince mana da  mu noma kadada  250,000.

 

A cewar Jakanta, kungiyar za ta noma kadada guda 50, 000, ce kawai, za a  kuma  rabar da sauran ga  kungiyoyin da suka nuna sha’awar su.

 

A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakuna a jihar Alhaji Yahaya Abubakar ya bayyana cewa, shirin zai samar da canji, musamman wajen kara habaka tattalin arzikin kasar nan.

Exit mobile version