Abubakar Abba" />

Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabon Tsarin Bunkasa Kananan Masa’anantu – Fashola

Gwmnatin Tarayya ta ta sanar da cewar, wanzar da sabon tsarin bunkasa kananan masana’antu dake kasar nan, zai bunkasa rayuwar yan kasar, musamman masu mastakaitan sana’oi. Ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ne ya sanar da hakan a lokacin a hirar damanema labarai a jihar Legas a ranar Alhamis a Abuja. Kamfanin dillancin labarai na kasa ya cewar, tsarin na kula da gine-ginen gwamnati, zai samarda ka’idojin gyra gine-ginen a daukacin fadin kasabaki daya. Har ila yau, an kuma dora mata nauyin kula da kadarorin gwamnatin ta hanyar bin ka’idojin da aka shinfida. Fashola ya ci gaba da cewa, Majalisar zartarwa ta kasa a ranar 9 ga watan Janairu,ta amince da Hukumar ta kula da gine-ginen na gwamnatin. Babatunde Fashola ya kara da cewa,ana kuma bukatar Hukumar ta horas da masu matsakaitan sana’oin a cibiyoyin da ake dasu a fadin kasar nan, ganin cewar, ana da karancin tsari na horaswa a kasar nan don ciyar da tattalin arzikin kasa. Babatunde Fashola ya sanar da cewar, hakan kuma zai sanya a kara samar da ayyukan yi, musamman ga masu matsakaitan sana’oin. Babatunde Fashola ya ce, bayana da ake dasu sun nuna cewar, an horas da mutane da dama akan sana’oin hannu da suka hadada, gyran Babura da kuma Kekuna.

Exit mobile version