Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Natasha A Kotu Kan Zargin Ɓata Sunan Akpabio Da Yahaya Bello
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Natasha A Kotu Kan Zargin Ɓata Sunan Akpabio Da Yahaya Bello

bySadiq
4 months ago
Natasha

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda aka dakatar daga wakiltar Kogi ta Tsakiya, a gaban kotu a Abuja bisa zargin yin ƙarya da ɓatanci.

An gurfanar da ita a gaban Mai Shari’a Chizoba Orji a Babban Kotun Babban Birnin Tarayya.

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo Ya Karyata Sauya Sheƙa Zuwa APC
  • Ba Za Mu Yarda A Yi Mana Ƙarfa-ƙarfa Ba – Ayatollah Ya Gargaɗi Amurka

Gwamnatin ta shigar da ƙara kan tuhume-tuhume guda uku da suka shafi zargin ɓata sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.

An ce zargin ya samo asali ne daga wasu kalamai da ake zargin Sanata Natasha ta faɗa a bainar jama’a, inda ta yi iƙirarin cewa waɗannan manyan ’yan siyasa biyu sun haɗa baki don kashe ta.

Ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen, an zarge ta da cewa a wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin, ta ce: “Yana cikin abin da suka tattauna a taron da Akpabio ya yi da Yahaya Bello a wancan dare, batun kawar da ni.”

Haka kuma, an ce ta ƙara da cewa: “Mu tambayi Shugaban Majalisar Dattawa, me ya sa ya janye jami’an tsarona tun farko, idan ba don ya sa a kai min hari ba? Ya ce a kashe ni, amma a kashe ni a Kogi.”

Gwamnati ta bayyana cewa waɗannan kalaman suna da nufin ɓata suna, kuma hakan ya saɓa da Sashe na 391 na Dokar Laifuka 89, Dokokin Tarayya na shekarar 1990.

Hukuncin laifin yana ƙarƙashin Sashe na 392 na wannan doka.

A wani tuhumar daban, an zargi Sanata Natasha da yin irin waɗannan kalaman game da Akpabio a cikin wata tattaunawa ta waya da wata Sandra C. Duru a Abuja, a ranar 27 ga watan Maris, 2025.

An ƙara tsaurara tsaro a wajen kotun, inda magoya bayanta da dama suka hallara don nuna goyon baya gare ta.

Daga cikin waɗanda suka halarta akwai mijinta, Emmanuel Uduaghan; tsohuwar Ministar Ilimi, Dokta Oby Ezekwesili; da mashahuriyar mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Aisha Yesufu.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamna Yahaya Bello, na cikin jerin shaidu da za a kira a shari’ar.

Sanata Natasha ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da tuhumar a yanzu.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa wata rana da ba a bayyana ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya

Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version