Gwamnatin Tarayya Ta Gurfanar Da Tsohon Shugaban Hukumar JAMB Gaban Kotu

Hukumar JAMB

Daga Idris Aliyu Daudawa

A ranar Talatar ce gwamnatin tarayya ta gabatar da tsohon magatakardan hukumar  (JAMB)ta kasa Farfesa Adedibu Ojerinde, a gaban wata babbar Kotun tarayya da ke Abuja, kan zarge-zargen da ake yi masa wadanda suka hada da zamba cikin aminci, ta  wasu  biliyoyin nairori.

Hukumar hana al’amuran da suka shafi karbar rashwata da cin hanci ta kasa, ita ce wadda ta gabatar da shi, akan aikata wasu laifuka ko kuma tuhume – tuhume wadanda suka kai 18, da kuma karkatar da kudaden gwamnati da suka kai sama da Naira miliyan 900.

An ce da ya aikata su laifukan a lokacin da yake magatakardan Hukumar Jarrabawa ta kasa (NECO) da  kuma ta shirya jarabawar zuwa jami’oi da kuma  manyan makarantu  na kasa JAMB.

Sai dai kuma ya musanta aikata laifukan da ake zargin sad a aikatawa, lauyan sa, Peter Olorunnishola (SAN) daga baya ya sanar da ita kotun, kan bukatar neman belin da ke da ita na shi inda kuma ya kara da cewa tuni ne aka nemi bukatar yin hakan dangane da shi neman belin na shi.

Duk da yake shi  lauyan da ke gabatar da kara, Ebenezer Shogunle, ya  bayyana cewa an sanar da shi kan al’amarin na neman shi belin, amma  kuma sai ya sanar da ita kotun akan rashin amincewarsa da bukatar yin hakan.

Hakanan ma ya nuna rashin amincewar sa,  akan wata bukatar cewa a kyale shi tsohon shugaban hukumar ta JAMB da kuma NECO ya ci gaba da belin da hukumar ICPC ta cashi can baya.

Bugu da kari kuma a wani gajeren hukuncin da ya yanke, alkalin kotun, mai shari\’a Obiora Egwuatu, ya bayyana cewa shi bai san da maganar yadda halin belin da ita hukumar ta ICPC ta bashi ba, wanda yake belin gudanarwar ne, don haka ya dage ci gaba da sauararen karar zuwa ranar Alhamis 8 ga watan Yuli, domin sauraron karar neman belin.

Sai dai kuma wani al’amari wanda kuma wannan na daban ne domin kuwa shi mai shari’ar ko kuma Alkalin ya ba da umarnin a ci gaba da tsare shi Ojerinde a cikin cibiyar gyara halin ka, har sai an saurari karar da kuma tabbatar da shi belin.

Ana dai tukumar shi tsohon shugaban hukumomin biyu Mista Ojerinde da karkatar da dukiyar jama’a da kuma yin bayanan karya, da dai sauransu, daga shekarar ta 2003 lokacin da yake magatakardan Hukumar Jarabawa ta kasa wato(NECO) har da ya  zuwa shekarar 2021.

A laifi na farko an yi zargin cewa, yayin da yake rike da mukamin magatakardan na NECO, ya yi amfani da matsayinsa ko mukamin  sa domin azurta  kansa ta hanyar “karkatar da zunzurutun kukade da har su ka kai Naira 27, mallakin gwamnatin tarayyar Nijeriya don amfanin kansa, don ya mallaki wani fili, a inda da aka sani da Tejumola House, Ikeja, Legas da sunan wani kamfani mai sunan Doyin Ogbohi , wani kamfani da kusan kamar mallakin sa ne a ciki. ”

A yayi da kuma su laifukan da ake zargin sad a aikatawa da suka hada da  na biyu, da kuma na uku, an  zargi Ojerinde da karkatar da Naira  bilyan 3, 811,876,230.10, ranar 16 ga Fabrairu, 2009 zuwa wani asusun bankin Zenith mai lamba: 1002833087 da kuma 1011265699 “da sunan JAMB-J. O. Olabisi.

 

Yayin da kuma a laifi na hudu da kuma na biyar ” Ana zarginsa ne da aikata  laifi lokacin da ya yi amfani da mukamin sa a matsayin san a magatakardan na hukumar  JAMB, inda ya aikata laifi ta bangaren bayar da cin hanci ga wani mutum mai suna Jimoh Olabisi Olatunde, wanda a asusun ajiyar kudin san a bankin Zenith da Stanbic IBTC Plc masu nambobi kamar haka: 1013583506 da 0022594599, da sunan JAMB- J. O. Olatunde, inda aka yi zargin ya karkatar da kudaden da suka kai  Naira 205,712,575.23 tsakanin  shekarun 2018 da kuma na 2019.

 

Daga karshe kuma shi laifi na shida wanda aka zarge shi da aikatawa an ce Ojerinde ya samu wani lokaci a tsakanin watannin Janairu da Fabrairu na shekarar 2014, ya ba wani abokin da suke aikata al’amuran rashawa da cin hanci, inda nan kuma aka yi zargin ya bada izinin biyan Naira milyan 486 ga wani kamfani  mai suna Messrs Pristine Global Integrated, ta asusun ajiya na bankin Zenith mai namba 1013701117 don samar da “kayayyakin rubuta jarabawa na JAMB wadanda suka hada da kalkuleta, fensir da kuma magogi abin goge rubutu, “wadanda jimillar sun zarce wadanda zai iya amincewa a kashe. Tun da farko dai an dakatar da shirin gurfanar da shi saboda bukatar daya nema  wani lokaci ta bashi dama wadda zata bas hi dama tare da ICPC, su samu damar kammala wani al’amarin daya shafi yarjejeniya da amincewa.

Exit mobile version