Gwamnatin Tarayya Ta Himmantu Kan Ceto Harsunan Nijeriya Daga Bacewa

Gwamnatin Tarayya, ta sha alwashin daukan duk matakan da suka dace na ganin ta ceto harsunan Nijeriyan da ke ta kara dushewa da nufin ganin ba su kai ga bacewa ba, inda take karfafa koyar da su a makarantun kasarnan.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ne ya fadi hakan ranar Talata a Abuja, lokacin da yake bude taron da aka yi wa lakabi da, “Enabling Writers: Bloom Software Training of Trainers workshop” wanda cibiyar ciyar da Ilimi gaba ta Afrika, (ADEA) ta shirya, tare da hadin hannun Kamfanin, ‘Global Book Alliance (GBA) da United States Agency for International Debelopment (USAID).

Ministan ya ce, wannan gwamnatin ta Shugaba Buhari, tana yin duk  abin da ya dace domin ta farfado gami da inganta al’adar karatu da rubutu a Nijeriya.

Don haka, sai ya kalubalanci marubutan kasarnan da su rika yin rubutun na su da harsunan kasarnan, wanda hakan zai kara samar da yawan littafan karatu da harsunan cikin gida.

Ministan, wanda Daraktan tsare-tsare da bincike na ma’aikatar ta ilimi, Dakta Chioma Nwade, ya wakilce shi, ya ce, hakan zai janyo hankulan matasan kasannan wajen iya karatu da rubutu da harsunan su, wanda hakan zai ceto harsunan Nijeriya da ma na Afrika daga bacewa.

Ya bayyana dagewan da gwamnatin tarayya ta yi wajen samar da wadatattu kuma isassun kayan karatun da suka dace a makarantu, ya ce hakan kuwa ba zai tabbata ba, ba tare da kayan aikin da suka dace ba, na littafai da sauran kayan aiki.

Babban mai jawabin na ADEA, din, Lily Nyariki, daga kasar Kenya, a jawabin na ta, ta bukaci gwamnatin kasarnan da ta habaka al’adar nan ta karatun littafai domin  karfafa al’adar ta rubutu da karatu a cikin kasarnan.

Ta yi jimamin sakamakon binciken da aka yi a yanzun haka, wanda ya nu na cewa, yara 15 ne suke fafutukar yin karatu da littafi guda a makarantunmu. Ta kara da cewa, ya kamata marubutan Afrika su samarwa da nahiyar matsayi ta hanyar yin rubututtukan na su da harsunan nahiyar.

Shugaban kungiyar marubuta ta kasa, (ANA), Denja Abdullahi, cewa ya yi, daya daga cikin babban matsalar marubutan na Afrika shi ne, ayyukan masu satar fasaha, wanda a cewarsa, hakan ya shafi ayyukan kungiyar marubutan na kasarnan matuka.

Ya ce, kungiyar shi a yanzun haka tana yin aiki tare da hukumar hana satar fasaha domin magance matsalar.

Exit mobile version