Daga Khalid Idris Doya Bauchi
Matasa maza da mata su dari uku 300 ne suka samu horo a fannoni sana’o’i daban-daban na sana’o’in dogaro da kai a jihar Bauchi a cikin shirin gwamnatin tarayya na habaka masana’antun kasar ta Nijeriya.
Babban Darakta a hukumar ta Industrial Training Funds na kasar Nijeriya, Mr. Joseph N. Ari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yaye matasan da suka samu nasarar samun horon na shekara ta 2017 wanda ya gudana a dakin taro na otel din Zaranda Bauchi a Litinin din nan.
Mista Joseph wanda samu wakilcin Zakariyya Jon Darakta a hukumar ta ITF a jihar Bauchi ya ce sun bayar da horo wa matasan ne a bangarorin sana’o’in daban-daban wadanda suka hada da aikin walda, dinki, harkokin gyaran hanyoyin tafiyar ruwa ‘famfo’ da sauransu a cikin shirinsu na NISDP.
Zakariyya ya bayyana cewar wannan horon dai na wata uku ne wadda matasan suka samu nasarar halartarsa daga gwamnatin tarayya domin kyautata musu rayuwarsu hade kuma da samar musu da aiyukan dogaro da kafafunsu, ya bayyana cewar dukkanin matasan an basu jari da za su ci gaba da riritawa domin tsayuwa da kafafunsu.
Ya bayyana cewar dukkanin daya daga cikin matasa dari ukun nan kowannensu ya samu kayyakin aiki a fannin da ya samu horo a karkashin shirin gwamnatin tarayya.
A ta bakin Darakta Janaral wato N. Ari ya ce shirin nasu domin su tabbatar da samar da hanyoyin dogaro da kai da kuma rage talauci ne a tsakanin al’umman “Mun bai wa matasan nan horo kan sana’o’in dogaro da kai, sannan kuma yadda suka kammalan nan kowa mun ba shi kayyakin sana’ao’i domin kowa ya je ya fara sana’a da kansa”. In ji shi DG.
Ya kuma bayyana cewar wannan yunkurin nasu na daga cikin nazarin da suka yi na yawaitar matasa masu zauna gari banza ne, ya ce a bisa haka ne suka ga ya dace suke gudanar da irin wadannan ba da horon domin bai wa matasan dama su fuskanci alkiblar da ta dace da su, da kuma rage talauci a tsakanin al’umma domin inganta sashin tattalin arzikin kasa.
- Ari ya ce, “Ina kira ga matasan da suka samu wannan damar su tabbatar sun yi abubuwan da suka dace a rayuwarsu domin gwamnati ta musu abun da ya dace wajen ganin sun samu abun yi, idan suka samu abun yi muna za mu samu zaman lafiya, domin idan matasa basu samu abun yi ba; to babu zaman lafiya, amma mun tabbatar wannan zai taimaki rayuwarsu da namu,”
DG din ya bayyana cewar, wannan mataki zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro da ake fama da su, a cewarsa yawancin wasu rikice-rikice suna samu asali ne a dalilin rashin abun yi ga matasa.
Da yake bayani kan aiyukan da hukumarsu ta ITF ta gudanar, ya bayyana cewar shekaru hudu kenan suna zakulo matasa domin basu wannan horon, ya ce sama da matasa dubu 11 ne suka ci gajiyar irin wannan tallafin na horarsawa da kuma kayyan aikin a jahohin 36 da suke Nijeriya, yana mai bayanin cewar za kuma su ci gaba da zakulo wasu matasan domin horas da su “muna addu’ar a wannan shekarar ta 2018 za mu samu zarafin inganta wannan aiyukan fiye da wadda muka yi a shekarun baya,”
Shugaban na shirin ITF ya yi amfani da taron wajen yin kira ga gwamnatin jihar ta Bauchi da ta shigo cikin shirin domin a samu cimma nasarar da aka sanya a gaba “Yanzu idan gwamnati za ta bayar da wani kwangila misali kamar na hada kujeru ko wasu fannoni muna kira ga gwamnati ta zo ta nemi wadannan yaran su yi mata domin sun kware sosai a bisa ababen da suka samu horo a kansu, muna kira ga gwamnati ta shigo cikin lamarin domin a taimaka wa matasan da suka kammala samun wannan horon,” a cewar DG Ari.
Shi ma a nasa jawabin, gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ESK ya bayyana cewar gwamnatinsa a shirye take ta ci gaba da taimaka wa matasa wajen ganin an shawo kan matsalar kashe wando da zaman rashin aikin yi a tsakanin matasa a fadin jihar.
Wanda ya samu wakilcin Kwamishinan ma’aikatar matasa da wassanin Pharmacy Ibrahim Madaki Sale ya ce “Gwamnatinmu na jihar Bauchi tana kokari sosai wajen ganin ta taimaka wa matasa ta fuskacin horar da su kan sana’ao’i. idan sun kammala samun horo kuma gwamnatin tana taimaka musu domin su samu zama da kafafunsu”. In ji wakilin gwamnan a wajen taron
Kwamishina a ma’aikatar matasa da walwalar yau da kullum ya bayyana cewar wannan asusun na ATF ya zo jihar a kan gaba la’akari da tabarbarewar matasa musamman kan rashin aikin yi tare da yin kira ga hukumar ta ITF da kada su yi kasa a guiwa game da irin aikace-aikacen na su.
Wasu daga cikin matasan da muka zanta da su sun nuna matukar jin dadinsu da bayyana cewar za su tabbatar da sun maida hankali wajen tsayawa domin yin amfani da ababen da suka koya na daga sana’o’in da aka taimaka musu a kai domin su ma su zama mutane na kwarai.
Ababen da suka wakana a wajen taron sun hada da baje kolin kayyakin da matasan suka kera da hannayensu da suka hada da rigunan dinkin zamani, kofofin dakuna da na shagona wadda matasan suka hada ta hanyar walda, da sauran kayyaki irin su ababen noma wato garma da makamantansu wadanda matasan suka kera, a lokacin da suke zagawa da shi don nuna masa kayyakin gwamnan Bauchi ya nuna jin dadinsa a bisa yadda ya ga kwazo da hazakar matasan a bisa tsayuwarsu don koyon ababen da suka dace da rayuwarsu, don haka ne ya bukaci matasan su ci gaba da nuna halin kwarai domin kasar ta samu kyautatuwa a kowani lokaci.
Yana mai bayanin cewar ta hanyoyin gudanar da abubuwan da suka dace ne kadai za samu kai wa ga nasara da kuma bai wa gwamnatin damar inganta rayuwar jama’a a kowani lokaci.