- Gwamnan Ya Bukaci Bude Filin Sauka Da Tashin Jiragen Saman Kano
Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
An jinjinawa kokarin Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa kirkira tare inganta hanyoyin gudunar da Kasuwanci a Jihar Kano.
Ministan Masana’antu, ciniki da zuba hannun jari na tarayyar Nijeriya, Mr. Otumba Richard Oni, da takwararsa, Karamar Mininsta Maryam Yala Katagum ne suka bayyana haka bisa yadda Gwamnatin Ganduje ta samar da dukkan abubuwan da ake bukata domin taimakawa a wannan bangare, kamar yadda babban daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.
An gudanar da wannan jawabi ne a lokacin bude Kamfanin Abinci da dangoginsa na Mamuda wanda ke cikin rukunin kamfanonin Mamuda dake rukunin masana’anta na Challawa a makon da ya gabata, dukkaninsu sun bayyana yadda Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwawmna Ganduje ta samar da kyakkyawan yanayin wuraren gudanar harkokin ciniki.
Katagum ta kuma bukaci al’ummar Jihar Kano da cewa karsu gaza wajen tabbatar da ganin suna amfana daga shirin matsakaita da kananan masana’antu, wanda aka tsara domin tallfawa harkokin kasuwanci a kasarnan.
Ta kara da cewa, gaskiya ne Jihar Kano da Legas sun samu kaso mai tsoka, idan akayi la’akari da yawan al’ummarsu. Hanyar da Gwamnatin Jihar Kano ke bi wajen habakawa tare da saukaka wuraren ciniki, “babu shakka Jihar ta cancanci dukkan goyon ba ake bukata.”
Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Gnaduje ya nuna farin cikinsa bisa goyon bayan da Jihar Kano ke samu daga Gwamnatin Tarayya kakashin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya jadadda cewa, “idan aka dubi kokarin da Shugaban kasa Muhammadu ke yi na samar da abubuwa da damammaki ga Jihar Kano da ingantaccen yanayin gudanar da harkokin kasuwanci, abun ayaba ne kwarai da gaske.
“Muna matukar godiya bisa yadda Shugaban kasa Muhammadu ke karfafa mana guiwa wajen tabbatuwar harkokin masana’antu a jiharmu mai albarka. Hakan zai taimaka waje sake farfado da matsayin Jhar Kano.” inji shi.
Daga cikin dalilan da ya lissafta, kan yadda muka aminta da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na nufin Jihar Kano da kyakkyawan alhari, a kokarin da ake na sake dawowa da Jihar Kano kan matsayinta, ta fuskar masana’antu da ci gaba da rike kambunta na cibiyar ciniki a arewacin kasarnan da ma makwabtan kasashen Africa, ya yi tsokaci da kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas daga Kano-Kaduna –Abuja (AKK) da kuma aikin titin jirgin kasa daga Kano-Katsina-Jibia har zuwa Maradin Kasar Nijar, da sauransu.
Sauran sun hada da, samar da katafariyar tashar jirgin kasa a Jihar Kano, Dambatta da Kazaure. Haka kuma tashoshin sauke kaya ta kasa wani harsahine da aka samar da zai habaka tattalin arzikin al’ummarmu ba tare da bata lokaci ba. Za’a iya tabbatar da jajircewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarin da yake na tabbatar da Kano cibiyar masana’antu.”
Hakazalika ya bayyana cewa, an ware sama da Naira biliyon 2 domin akin tashar wuraren sauke kaya na doron kasa. “domin tabbatar da haka. Mun samar da hanyoyi da gina wasu hanyoyin a wasu wurare da ake aikin yi a ahalin yanzu. Muna kuma fatan cewa, wannan aiki za’a kammala shi a karshen wannan shekara,” inji Ganduje.
“Mun yi magana da kamafanonin jiragen sama, misali Emirate Airline sunzo nan sau da dama inda suke nuna aniyarsu na fara gudanar da harkokinsu daga Kano. Sakamakon haka ne, muka gudanar da wasu aikace aikace domin inganta harkokin tsaro a filin sauka da tashin jiragen saman.”
A nasa bagaren shugaban kungiyar masu masana’antu na Kasa (MAN) Injiniya Mansur Ahmad ya nuna farin cikinsa bisa yadda Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da hankali kan tallafawa harkokin kasuwanci, tare da gudunmawar Gwamnatin Tarayya.
“Muna godiya kwarai bisa yadda Gwamnatin Jihar Kano ta samar da kyakkyawan yanayin gudanar da harkokin kasuwanci. Yanyin da kuma ake kan aikin samar da ingantattun tsare tsare ga masana’antu masu zaman kansu, amfani da abubuwan da ake sarrafawa acikin gida shi ne abinda Gwamnatin ke kara himmatuwa akansa,” inji shi.