Umar A Hunkuyi" />

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Daidaita Jinsin Maza Da Mata Ta Fuskar Aikin Gona

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shiri na samar da daidaito a tsakanin jinsin maza da na mata a kana bin da ya shafi sha’anin noma domin ragewa mata wahalar da suke sha na bin hanyoyi domin cimma manufar shirin karnin nan na 2030 da samar da tsaron abinci a kasar nan.

Da yake Magana a wajen kaddamar da shirin jiya a Abuja, Ministan aikin gona da raya karkara, Alhaji Muhammad Sabo Nanono, ya yi nuni da cewa tsarin an shirya shi ne domin bayar da gudummawa wajen cimma farfado da ayyukan noma da wannan gwamnatin ta sanya a gaba.

Ya ce, “Duk da mahimmancin gudummawar da mata suke bayarwa a sashen na noma, amma ba a faye ganin gudummawar da suke bayarwa yanda ya kamata ba.

“Mata su ne kashi 50 na yawan al’ummar Nijeriya su ne kuma suke dauke da nauyin kashi 70 na ayyukan noma, kiwo da kashi 60 na abin da ya shafi samar da abinci.

Amma suke da kasa da kashi 20 na albarkatun noma, wanda wannan babbar matsala ce da kuma tauye su a sashen na noma, wannan kuma shi ne dalilin kaddamar da wannan shirin mai mahimmanci.

A cewar shi, ci gaban kowace kasa yana da bukatar sa hannun maza da mata ne, baya ma ga abin da ya shafi adalci na yin daidaito da bayar da dama iri guda ga dukkanin ‘yan kasa.

Ya bayyana cewa, tsarin zai karfafa tare da tabbatar da ana kula da daidaiton jinsin maza da na mata a kan dukkanin shirye-shirye ta yanda maza da matan za su rika samun dama iri guda domin a cike gibin da ke tsakani a sashen na noma.

Ya bayar da tabbacin samar da ababen more rayuwa da karfafawa ga mata da maza a sashen na noma.

 

 

 

 

Exit mobile version