Abubakar Abba" />

Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Gonakin Zamani Biyu A Jihar Edo

Gonakin Zamani

A bisa kokarin Gwamnatin Tarayya na habaka tsarin aikin noma a kasar nan, Hukumar Bunkasa Kogin Owena (BORBDA), ta kadanar da ayyuka gonakai biyu na zamani a yankunan Okpe da Uneme Nekhua a karamar hukumar Edo cikin jihar Edo.

A jawabinsa a wurin kaddamar, Manajin Darakta na Hukumar ta BORBDA Saliu Ahmed ya ce, an kara farfado da gonakan biyu ne domin habaka fannin aiki noma da kuma kara samar da wadataccen abinci a kasar.

Manajin Darakta na Hukumar ta BORBDA Saliu Ahmed ya ci gaba da cewa, gonakan biyu an kara fadada su domin noma kadada 100 a ko wacce kadada daya, inda ya ci gaba da cewa, an kuma samar wa da aikin kasuwar sayar da amafanin da aka noma a gonakan da sauaransu.

Saliu Ahmed ya kara da cewa, ayyukan da za a gudanar a ginakan za su taimaka wa manoma wajen sanin dabarun noma na zamani tare da gudanar da bincike man fannin akin noma, inda ya ci gaba da cewa, ayyukan za su kuma taimaka wajen habaka samar da abindi a kasar nan, musamman kan fannin noman Togo, samar da sauran amfanin gona, abincin dabbobi da kuma tabbatar ana kare yin asararw amfanin gona.

A cewar Manajin Darakta na Hukumar ta BORBDA Saliu Ahmed, za a kuma zabo wasu matasa daga cikin alumna wadandaw za a ba su horo a gonar Songhai Porto Nobo, da ke a kasar Jamhuriyar Benin.

Manajin Darakta na Hukumar ta BORBDA Saliu Ahmed ya ci gaba da cewa, aikin a yanzu anaw kan fara yin gyare-gyare ne, kuma ana bukatar alummar da ke a yankin su ne za su kula da aikin.

Shi ma a na sa jawabin a wurin kadamarwar, mai lura da aikin wanda kuma ya kasance Dan Majalisar Wakilai da ke wakiltar mazabar Akoko Edo daga jihar Edo a karkashin inuwar jamiyyarsa ta APC Peter Akpatason ya bayyana cewa aikin ya na daya daga cikin yunkurin gwamnatin Tarayya na kirkiro da ayyukan yi ta hanyar aikin noma a daukacin fadin kasar nan, inda ya ci gaba da cewa, aikin zai kuma taimaka wajen gudanar da bincike kan fannin noma, gudanar da yin kiwo da kuma samar da kasuwa ga amfanin gona.

A wani labarin kuwa farashin Shinkafa da ake noma wa a jihar Taraba, bisa binciken da aka gudanar, ya nuna cewa, ya ragu, inda ake sayar da buhu mai nauyin kilo dari kan naira 10,000 zuwa naira 10,500 sabanin yadda ake sayar wa a baya, daga naira 14,000 zuwa naira 15,000 a satin da ya wuce.

Har ila yau, farashin wasu amfanin gona da ake noma wa a jihar, ya ragu, inda aka ruwaito cewa, buhun Shinkafa da ake noma wa a jihar mai nauyin kilogiram 100 ya ragu, inda a yanzu, ake sayar buhu kan naira 27,000 sabanin a baya da ake sayar wa kan naira 37,000a satin da ya wuce.

Bugu da kari, bisa binciken da aka gudanar ya nuna cewa, yan na kama na amfanin tuni sun bazama domin saye Shinkafar domin boye ta domin ta kara kudi.

Akasarin kasuwannin da ke a yankin Lau, Mutum Biyu, Garba-Chede, Tella da kuma Maihula ana samun masu sayenta ‘yan kadan.

Wani manomi a karamar hukumar Bali Malam Ibrahim Adamu an ruwaito ya ce, farashin Masara Wake, Waken Soya da sauransu, farashin su ya ragu.

Manomin Malam Ibrahim Adamu ya ci gaba da cewa, buhun farin Wake mai nauyin kilogiram 100, a yanzu ana sayar da shi kan naira 14,000 sabanin kan naira 19,000 a baya, inda yaci gaba da cewa, buhun Masara mai nauyin kilogiram 100 a yanzu ana sayar da shi kan naira 9,000 zuwa naira 10,000 sabanin kan naira 13,000 a baya.

Exit mobile version