Gwamnatin Tarayya Ta Kai Daraktoci 5 Na Cibiyar Wasanni Kotu

Daga Umar A Hunkuyi

Gwamnatin tarayya ta maka daraktoci biyar na cibiyar wasanni ta kasa da ke Iganmu-Legas, gaban babban kotun tarayya ta Legas, bisa zargin su da karban Naira 500,000, daga hannun wani dan kwangila.

Wadanda ake zargin su ne: George Ufot Ukanta, Abiodun Abe, Femi Joel, Ndubuisi Nwogu da matar wani janar din soja mai ritaya, Uwargida Doris Okafor.

Mutanan biyar kamar yadda takardar shigar da karar ta nuna, ana zargin su ne da karban cin hancin Naira 500,000, a ranar 16 ga watan Janairu 2017, daga wani kamfanin ‘yan kwangila mai suna, ‘Market Edecution Solution Limited,’ wanda yake yi wa gwamnatin tarayya wani aikin kwangila a wurin na su.

Sai dai, gabatar da su din gaban kotun ya sami cikas, saboda rashin kasancewar Uwargida Okafor din, wacce aka ce an kwantar da ita a asibitin Sojoji na Ikoyi-Legas, kan rashin lafiya.

Lokacin da aka kira karar ranar Litinin, lauyan da ke kare wadanda ake zargin, Adamu Mohammed, ya shaida wa kotun cewa, wacce ake tuhuma ta biyar, Uwargida Okafor, ta zo kotun da safiyar ranar, amma an garzaya da ita asibitin Sojojin kan rashin lafiya.

Lauyan ya ce, a kafafen yada labarai ne suka ji tuhumomin da ake masu, sai a harabar kotun ne kuma aka ba su kwafen tuhumomin da misalin karfe 2 na rana.

Lauyan kuma ya shaida wa kotun, sun shigar da bukatu biyu, daya na kalubalantar kotun kan ba ta da hurumin sauraron karar, dayan kuma ta neman belin wadanda ake tuhuman.

Sai dai, ya roki kotun da ta sanya wata rana domin ya sake gabatar da wadanda yake karewar, kasantuwar rashin Uwargida Okafor.

Da yake mayar da martani, mai gabatar da karan, Dakta Colsus Ukpong, cewa ya yi, Uwargida Okafor kin karban takardar karar ta yi. Ya ce, maganan rashin lafiyar na ta duk wata hanya ce ta kaucewa gabatar da ita gaban kotun.

Colsus Ukpong, ya ce, yana shirin ya gabatar wa da kotun bukatar kotun ta sanya a kamo Uwargida Okafor din ne.

Daga nan mai gabatar da karan ya nemi kotun da ta umurci lauyan wadanda ake karar da ya karbar wa Uwargida Okafor na ta kwafin takardar karar a madadin ta.

A nan ne Lauyan kare wadanda ake tuhuman ya karbi takardar karar na ta a madadin ta.

Sai Mai shari’a, Sule Hassan, ya daga shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Mayu domin a sake gabatar da su.

Exit mobile version