Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Rashin Biyan ‘Yan Taratsin Neja Delta Alawus

Published

on

Gwamnatin tarayya ta karyata zargin rashin biyan tsaffin ‘yan ta’addan Neja Delta 61 wadanda suke cikin shirin afuwan Shugaban kasa, kudaden alawus din su na wata-wata.
Mista Murphy Ganagana, kakakin wa mai baiwa Shugaban kasan shawara, kan abubuwan da suka shafi yankin na Neja Delta, wanda kuma shi ne shugaban hukumar ta PAP, Charles Dokubo, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya yi nu ni da cewa, wani kamfani a madadin wasu mutanan da ba a san ko su wane ne ba, da suke riya cewan su ma masu hankoron ne na Neja Delta, sun rubuta takardar koke zuwa ga Kakakin Majalisar wakilai ta kasa, Yakubu Dogara, a kan hakan.
A cewar Gangana, masu koken sun hada da sunayen wasu mutane 61 wadanda a cewar su duk suna daga cikin mutanan da aka zambata, suna zargin ofishin yin afuwar da kin biyan su kudaden alawus din na su da kuma karkatar da kudaden da aka kebe wa tsaffin ‘yan ta’addan domin ba su horo na musamman da kuma karfafa su.
Ya kara da cewa, “Da karban koken, wanda aka aike wa da Farfesa Dokubo da kwafi, nan da nan sai Farfesan ya sanya a binciki zargin.
“Da fara binciken sai lamarin ya so ya zama almara, inda wasu daga cikin wadanda sunayen na su ke cikin jerin mutane 61 din suka nu na ba su da masaniyar an rubuta koken. Daga cikin su akwai Amatelemowei, wanda sunan sa ne na farko a cikin jerin sunayen 61 da ake zargin an hana su kudaden alawus din na su.
“Sai dai, da muka bincika a ofishin yin afuwar na Shugaban kasa dangane da sunayen mutanan 61, mun taras da cewa, mutane 40 cikin su suna cikin kashi na farko ne, sa’ilin kuma da mutane 20 a cikin su suke cikin kashin shirin yin afuwar kashi na biyu, mutum guda kuma daga Jihar Akwa Ibom, ba shi a cikin shirin afuwar na shugaban kasa.”
Kakakin na Dokubo ya yi nu ni da cewa, mutane 60 da suke a cikin jerin sunayen duk suna cin gajiyar shirin yin afuwar, 33 ma daga cikin su tuni sun sami horo a fannuka da dama, suna sauraron a karfafe su ne kadai, sauran kuma suna kan layi ne a halin yanzun.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: